Wannan mataki shi ne na jawo hanlakin jama’a, sarakuna da kuma jami’an hukumomin kauyen game da karɓar kuɗin haraji, tun da wannan shi ne abu na farko game da ci gaban kwamin. Magajin garin Dankatsari dai ya gane muhimmancin shi.
Lokacin da ya fara aiki a watan Yuli 2011, bayan da Prefet na Dogondusti ya yi rikon kwarya magajin garin Dankatsari aka tabbatar da Prefet na Dogondutsi, ya gano cewa, kuɗaɗen da aka samu a kasance € 8,000 ne yayin da kimanin kasafin kudin shekara ta 2011, sun kai € 110.500. tun lokacin yake gudun shiga a cikin irin wannan halin.
Sakamakon da ya samu su ne :
- 2011: hango : € 110.500, abun da aka samu : 130 00 €
- 2012: hango: € 116.500, abun da aka samu: € 119.200
- 2013: hango: € 122 500, abun da aka samu zuwa 8 ga watan Yuli: € 83,000 (an yi ragowa saboda a lokacin, kamfanin wayar nan mai suna Airtel bai biya kuɗin kamashon garin ba).
An yi horo a kan hanya janyo ra’ayoyin jama’a da kuma muhimmancin karɓar kuɗin haraji ranar 9 da 11ga watan Janairu 2014 (a Gofaua da Ɗankatsari) tare da halitar jami’an hukuma da kuma shugabannin garuruwa 48 da abin ya shafa daga baya kuma an yi ziyaru cikin garuruwa goma sha biyar waɗanda ba a samun kuɗin haraji sosai ba.
Wannan mataki ya ci gaba a 2015 da kuma 2016.
A shekarar 2020, da farko dai aikin na samar da rangadin wayar da kai ne, a kauyukan karamar hukumar wadanda suka fi kowa jinkiri wajen biyan haraji. To, Magajin garin Dankatsari, da ya lura da cewa jama’a suna biyan harajinsu yadda ya kamata kuma alhakin rashin biyan harajin yana kan shugabannin garin ne, ya shirya taron shugabannin kauyukan da kwamun da ke jinkirin biyan kudi haraji.
Taron farko ya gudana ne a ranar 15 ga Fabrairu, 2020. Ya haɗa shugabannin ƙauyuka 57, da mayan ƙaramar hukuma, shugabannin ƙauyuka da ƙungiyoyi da kuma shugaban sashen. Jawaban da aka gabatar, sun amince da maida hankali kan wajibcin biyan haraji da kuma amfanin sa wajen bunkasa yankin karkara sannan kuma sun yi magana kan hadarin da ke tattare da wadanda ke wawuren wadannan kudaden jama’a. Taro na biyu wanda aka shirya a watan Nuwamba bayan girbi, an jinkirta shi saboda kalandar zaɓe, sannan kuma saboda COVID. A ƙarshe an shirya shi a ranar 6 ga Maris, 2021, tare da halartar shugabannin ƙauyuka 59 da na ƙaramar hukumar, da shugabannin ƙauyuka da ƙungiyoyi da kuma shugaban sashen.