Lugu yana fama da tsanantattar matsalar ruwa. A shekara ta 2002, pampon murtsatse 1 ke akwai ; sai yawan lalacewa, duk da yawan gyaran da ake yi mashi ; kuma rijiya guda ce mai zurfin metir 80, wadda mazamna garin da makiyaya suke yin amfani da ita ; ita ma tana yawan yashi. A wasu lokutta ma, ruwan tabki ne mutanen garin suke sha.

Ga yadda matakan farkon suke

Kayan aikin jan ruwa

A shekara ta 2004, Tarbiyya Tatali ta bada taimako don gyaran rijiyar, da sayan kurar jan guga, da shanu masu ja. Ba a samu sulhu wajen kafa kwamitin tattali ba, tun da shugaban ya rasu. A halin yanzu an yashe rijiyar, kuma an kawo jakai maimakon shanu.

Gyaran pampon murtsatse

Ruwan pampon masu tsabta ne, tatattu ne ; su kuwa ruwan rijiyar da ake yin ban ruwan bisashe da su, bai dace mutane su sha su ba. cinikin da aka yi wajen sayar da littafi mai suna ‘’Lugu da sarauniya’’ ya ba da damar gyara pampon a ƙarshen shekara ta 2007.

A ƙarshe bana wato 2012 za a ƙafa wurin ɗaukar ruwa mai pampo biyu.

Wurin samun ruwa na Lugu

Garin Lugu ya samu ranar 12 ga watan fabrairu 2013, wurin samun ruwa na kanta.
A wurin dai akwai, wani ‘karamin shaton ruwa, da kankare, wato wurin ‘daukar ruwa mai pampo biyu, da pampo biyu da aka kafa, ‘daya cikin makarantar, ‘daya kuma cikin gidan lafiya.
An yi babban biki ranar 20 ga watan febrairu 2013. Parepe na Dogondutsi, da magajin garin Dankassari, da daraktan mai kula da sha’anin ruwa “hydraulique” na jihar Dosso, da na Dogondutsi, da wakilai hu’du na RAEDD, da mai ‘daukar hoto, da talabijin ta jihar, da sarakunan garurukan jihar, da wanda ya aikata aikin nan, da ‘yan garin Lugu, dukansu, suka taru bayan Sarauniya Aljima don muna murnarsu.

Fim [Ruwa falala Lugu->https://vimeo.com/268609761 yana nuna canji da samun ruwa ya kawo a cikin rayuwar garin.