An kammala wannan mataki.

‘’Rendez-vous d’Afrique’’, shi ne ake ce wa saduwa da Afirika a cikin harshen hausa, harshen da ya yi yaɗo a Afirika ta Yamma, kuma da ake yin amfani da shi a Ɗankatsarin Nijar , gari mai hulɗar dangantaka da Cesson Sévigné.

Saduwa da Afirika, wasu shagulgulla ne na nuna al’adu da za a yi a wani lokaci da aka ke’be cikin shekara ta 2010 zuwa 2011 a garin Cesson-Sévigné.

Hukumar sadarwa da ta al’adu na birnin Cesson, da ƙungiyar AESCD, da kuma fannin ‘’Silma’’ na sévigné suke shirya shagulgullan.

Ƙungiyar ‘’Isa Ceso’’ ta kiɗi da waƙe-waƙe, da Zara Musa a fage.

  • Ranar juma’a, 18 ga watan ’faburairu a ƙarhe 8 da minta 30 na dare, Carré Sévigné (Parc de Bourgchevreuil, Cesson-Sévigné)

Ƙungiyar ‘’Isa Ceso’’ da harshen zabarmanci, kenan ‘’Le long du fleuve’’ da ’faransanci, ko kuma ‘’Bakin gulbi’’ da hausa, tana yin garwayen salon kiɗi mai ƙayatarwa.

Zara Musa KZM, shahararriyar mawakiya ce da ta yi suna a fannin waƙe-waƙen mata a Afirika ta Yamma. Tana yin waƙoƙi masu tada tsime, da wani salon da ake kira rap, tare da yin kokowar magance da matsalolin da suka shafi al’umma, da yaƙar rishin adalci da ake yi wa mata, har da wanda Afirilka Baki ɗaya take fuskanta. Ƴan Ƙungiyar kiɗi mai ƙumshe da mutum 3 ta ‘’Ganga Mise’’ za su yi rakiyar ta.

Zara Moussa
Zara Moussa

Nuna filim mai sunan ‘’un homme qui crie’’

  • A ranar Littanin 14 ga watan ‘faburairu a ƙarhe 8 da rabi na dare, a gidan silmar ‘’Le Sévigné’’.

Malam Mahamat-Saleh Harun ne ya yi wannan filim ɗin, kuma ya samu tukwicin farko ga bikin nuna finafinai na ‘’Cannes’’ a shekara ta 2010.

Biki 3 na nunin al’adun

  • Nunin finafinai na Afirika daga ranar 16 zuwa 22 ga watan ’faburaru a ɗakin silmar ‘’Le Sévigné’’.

Hotuna 15 na Ƴan wasan Afirika da aka ɗauka a lokacin bikin nuna finafinai ‘’FESPACO’’ na birnin wagadugu (Burkina Faso).

  • Matan Ɗankatsari, a cikin watan Apirilu zuwa Mayu na 2011, a cibiyar al’adu ta ‘’Bourgchevreuil’’.

Hotuna ne da abubuwan shaida. Wani aiki ne da birnin Cesson tare da ‘Kungiyar AESCD suka gabatar da hotunan matan Ɗankatsari, waɗanda Jean-Pierre Estournet da Abdoul Aziz Soumaila Suka yi.

  • Issa Ceso, a cikin watan Apirilu zuwa Mayu na 2011 a ‘’Bourgchevreuil’’.

Wani rahoto da Jean Pierre Estournet da Abdoul Aziz Soumaila suka nuna bisa maza da mata, da yanayin bakin gulbin Nijar da ake kira Isa Beri (Babban Gulbi) cikin harshen zabarmanci ko sanwayanci, tun daga birnin Yamai na ƙasar Nijar har zuwa Segu a Ƙasar Mali. Tsawon wata 1 suka ‘dauka suna bin garuruwa da tsibirran gulbin suna yin hotuna tsakanin garin Tilaberi, da Gawo, da Buren, de Bamba, da Tambuktu, da Sauran su.