Birnin Cesson-Sevigne yana da rarraba hadin kai ta yarjejeniyar da Dankatsari a Nijar, ta danƙa wa kungiyar hulda ta Cesson-Dankatsari aiwatar da ayyukan. Wannan karamin matani don amsawa ga tambayoyi mafi yawa na yan Cesson.

Me ya sa yake da muhimmanci a taimaka wa ci gaban Nijar?
Wannan ƙasa ce sau da yawa akan manta da ita (an fi taimako Mali, Burkina Faso, Senegal).
Manufofin: kullawa da yawan jama’a a cikin kasar tare da samun rayuwa mai kyau, taimakawa wajen gina wannan sabuwar dimokuradiyya, horon mutane domin su kula da kansu

Cikin wane irin hali na siyasa ake a Nijar?
Nijar jumhuriya ce, mai shugaban kasa, da majalisa, da dokokin kasa da kuma ‘yan hukuma. 2016 shekarar zabe ce shi ya sa ake samu tashin hankali da haddasa yanzu.

Kuma yaya ake wajen yanayin tsaro?
Kafin Faransa an kai wa Nijar hare-haren bakin wake. Akwai rashin kwanciyar hankali wajen makwabta da dama (Libya, Nijeria, Mali). Nijar tana taimako ’yan gudun hijira masu gudun Boko Haram.

Wajen addini fa?
Mafi yawan mutamen ta Musulmai ne, amma akwai wasu addinai.
A Dankatsari misali akwai wani gida na addinin crista.

Ko da akwai matsaloli na kabilanci?
A’a. Akwai cudanyar mutane da yawa masu kabilu daban daban a Nijar : ‘yan gari masu jin maganar Hausa ko Zabarmanci, masu yawon kiyo (Fulani, Abzinawa) kuma akwai aure da yawa tsakanin kabilolin nan. Gwamnati na aiki sosai wajen hadin kai mutanen Nijar.

Wane harshe ake amfani da shi wajen aiki?
harshen Faransanci amma akwai harsunan Afirka da dama.

Me ya sa birnin Cesson-Sevigne-yake da la’akari na musamman da garin Dankatsari?
Domin akwai wani rokon bukata ta magajin garin Dankatsari. Ma’aikatar magajin Cessson-Sevigne ta amsa da cewa yana da muhimmanci a taimaka wa wannan sabuwar kwomun ta garin Nijar don ta samu tsarin kanta. Hallarar ƙungiyar, RAEDD, wadda ke hulda da ta AESCD cikin Tarbiyya Tatali-ya sa a samu wani hukunci hujja.

Nawa ne yawan mutanen Dankatsari?
kusan mutane 80,000 ne cikin kauyuka talatin da ta hallara
Makarantu nawa ne? Fiye da ɗari
Likitoci nawa ne? ɗaya
Asibici nawa ne? hudu

Mene ne hulɗa ta haɗin gwiwa ?
hadin kai ne na yarjejeniyar tsakanin kananan hukumomi biyu na kasashe daban-daban, wani ɓangaren siyasar kasashen waje da manufofin na Faransa ne. Hukumar tana iya gudanar da ayyukan kai tsaye ko kuma wata kungiya ta dauki wakilcin ta.

Shin akwai banbanci da amintaka tsakanin gari biyu?
A’a, doka ɗaya ce ta 6 ga watan Fabrairu 1992,wadda ake aiki da ita. Ana maganar hadin gwiwa a lokacin da ake taimakon kudi zuwa kasashe masu tasowa. An yi wata doka ran 2 ga watan Fabrairu 2007, don amincewar da matakan rarraba hadin gwiwa na hukumomi don daukar matakai na ci gaban taimako ba tare da iyakancewa ta fannin wata gwaninta.

Mene ne muhimmancin AESCD?
AESCD ita ce ke gudanar da ayyukan rarraba hadin gwiwar garin Cesson-Sevigne da Ɗankatsari. Har ila yau, tana da wani aiki na baza labarai don bunkasa kasar Nijar da Ɗankatsari a Cesson-Sevigne, wajen makarantu, kazalika kuma da nune-nunen, mahawarar game da fim. Muna rubuta neman taimakon kudade da rahotannin aikace-aikace da kuma na kudi.


Tun shekara ta 2011, ba’a iya samun zuwa Dankatsari, wadanne hanyoyin kuke amfani da su wajen saka idanu cikin tsarin ayyukan a can?

Mun aiwatar da wani tsarin na rubuta rahotannin kowane wata, shugaban rarraba hadin gwiwa da akantan RAEDD ke rubuta su, kuma muna musanyar imel da kuma wayar tarho. Ba mu iya zuwa Dankatsari amma muna zuwa birnin Yamai kowace shekara inda muke haduwa da duk waɗanda suke da alhakin ayyuka daban-daban domin yin nazari da su.

Wa yake tsara ayyukan a can?
Majalisar Dankatsari ta tsara ci gaban shirin bisa ayyukanta dangame da mahallunan gwaman Nijar. Ma’aikatar magajin garin Dankatsari da RAEDD da AESCD, ke tsara ayyukan. Sai a kai wa garin Cesson-Sevigne da hukumomi daban-daban ƙaddamar da shawarar ayyukan nan don samun kuɗin
gudanar da su.

Su mene ne sassan hidimomin nan?
A fagen samun ruwa, da makamashin kayan a wurare kamar (likitoci, makarantu), taimaka wa mata, da muhalli, da karfafa wa ma’aikatun magajin gari, da dai sauransu ... ko da yaushe tare da horo da kuma a fanin zahiri. Ana la’akari wayen mata da maza wurin horon. Mata sun gamsu sosai da ayyukan da ake aiwatar da. Ana nazarorin ayyukan da ake gudanar da (samun ruwa, bankunan hatsi da injin nika hatsi, da kuma noma) don gano bunkatu da yin ayyanar manyan al’amurra.

Wadanne kungiyoyi ke kawo taimakon kudi don gudanar da ayyukan Dankatsari kuma har kasafin kudi nawa ?
taimakon garin Cesson-Sevigne (euro 12 000 a kowace shekara a 2015-16-17) shi ne masomin ayyukan nan. An ruba ta da wani taimako na MAE (garin Cesson-Sevigne ke yin takardun menan kudin). An samu taimakon wasu kudadde daga wasu hukumomin (sashen). Wajen bangaren ruwa akwai tallafin daga wata ma’aikata mai sunan kungiya ta ruwa ta Loire Bretagne da CEBR (Collctivités Eau du Bassin Rennais). Wajen bangaren makamashi kungiyar jiha ta Energy 35. Muna da kuma kudin mu (membobinmu, kyaututtuka, kudin saide saidan kayan hannu na Nijar). A 2015 kasafin kudin mu ya kai wajen euro 90 000.

Yaya ake tsakanin hukumomin masu ba da kudade da Ɗankatsari ?
Aiki AESCD dai gaiya ce ake. Ana aika kudaden da aka samu gidan kudin RAEDD a Yamai wanda za ta dauki 10% na gudanar da ayyukanta (hayar ofishoshinta, albashi mai kula da kudin, da na mai lura da rarraba hadin gwiwa, kudin gyaran motoci). Idan an tsara wani aiki a Ɗankatsari, sai a tsamon adadi kudin a aika zuwa ga reshen RAEDD. RAEDD tana iya kashe kudin ko kuma ‘yan ma’aikatar majagin garin Dankatsari. Daga bayan sai a aiko mana takardun shaidar adadin kudin da aka kashe.

‘Yan Nijar suna kawo taimakon su na kudade wajen yin ayyukan?
E’e, a wasu siffofin (hallara wajen kawo kudade, aiki wanda bai da albashi). Ga misalai biyu : Gwamati na kawo taimako 40% na kasafin kudin domin mataki « sayen amalenkan ungozumai” aiki dai, yanzu ana yin sa da biyen rancen kudade na ungozumai wanda yake ba da damar sayen sabin amalenke.


Shin gwamantin Nijar na daukar wani abu bisa kadaden da ake aikowa?

A’a misali don fannin kuzari kayan aikin da ake aika ba’a biya masu kudi kwasta.

Me ya sa taimakon kudade na birnin Cesson-Sevigne yake da muhimmanci?
Taimakon ainihi na Cesson-Sévigné shi ne tushen mu wajen neman goyon bayan sauran abokai. Sauran kungiyoyin suna bukatar a haɗa kudade kungiyoyi kuma suna la’akari da gudunmawar da garin Cesson-Sevigne take baiwa. Misali MAE (ma’aikata mai kula da kahashen waje)na tallafawa da ruɓa taimakon Cesson. Za mu iya cewa euro 1000 da Cesson ke baiwa na sa a samu euro 8000 na taimakon wasu kungoyoyi, inda aka kara da kudaden Nijar euro 12000 wadanda ake aiki da su can.

Tun shekara 2009 ake aikin rarraba hadin gwiwa. Shin, an samu ci gaba? Matsalolin?

Akwai ci gaba sosai. Rahotannin da ake aiko mana na nuna haka. Alal misali garin Dankatsari ya kafa wata ma’aikatar magajin gari don na’ura mai aiki da karfin ruwa da kuma dauka wani mai kulawa da shi, ya inganta biya haraji. An fi samun matsaloli wajen karuwar yawan mutane, wanda ke kawo har kullum karin bukatun sabin kayan aiki (samun tsabtatun ruwa, makarantu, da kiwon lafiya).

Mene ne sakamakon ayyuka game da aikin rarraba hadin gwiwa?
A fagen samun ruwa, da zamantakewa an tsara wani na’ura mai aiki da karfin ruwa,an kafa wuri samun tsabtatun ruwa, kuma an gyara biyu, an gyara rijiyoyi tara, an horar da membobi 250 na COGES da masu gyara 100. An inganta wurin samun ruwa na mutane kamar 15 000 da suke rayuwa a cikin kwaminonin. Game da wasu bangarori za a samu wani cikakken rahoto da AESCD za ta gabatar da a ISS shekarar 2016.

Har yaushe za a ta ci gaba da aikin rarraba hadin gwiwa?
Rarraba hadin gwiwa dai abu ne mai daukar dogon lokaci. Ana yin ayyukan bisa bukatun mutane. Ana nazarin yawan kudi da ake kashewa na shekaru uku (Tattaunawar Majalisar ma’aikatar magajin gari ta shekara 2017 don adadin kudi na shekaru gaba).

Mene ne sha’awar aikin rarraba hadin gwiwa da Dankatsari yake gabatar wa a Cesson?
Sha’awarwarin dai suna da yawa: bayanai da horo (wayewar kai ga duniya) don yara da al’uma duka, al’adu (nune-nunen, fim), ganuwa (yanar gizo na ma’aikatun biyu (MAE da na Horo), na yankin wurin samun ruwa da dai sauransu ... game da karin na garin Cesson-Sevigne da Tarbiyya Tatali-).

Mene ne tsare-tsaren ku na shekarar 2016?
A Dankatsari za mu ci gaba da shirye shiyan ayyukan da fatan cewa sabon magajin gari zai zama kamar wanda ya rigaye shi a matsayin baya. A Cesson muna da alhakin yin tsare tsaren na makon taimakon juma na duniya, muna nune nunan hotuna, nunin wani ɗan gajeren fim “Lugu ta samu ruwa” wanda wasu kwararrun yan fim na Nijar suka yi ba da amsar kudi da yawa ba. Muna tarbar mutun ɗaya ko biyu masu tahowa daga Nijar.

version .pdf du document