An kammala wannan mataki.

Zaman cuɗayyar juna

Tun shekara ta 2006, ɗalibai ’faransawa maza da yawa, sun shawarce mu cewa suna son yin ayyukan ƙwarewa a Nijar, dangance da fannin karatun da suke yi, ko kuma a lokacin hutunsu. Su ne suke ɗaukar nauyin biyan balaguronsu, mu kuma muna sulhunta masu wajen samun gidan haya da abinci cikin rahusa. Tun wannan lokacin ne, har masu ritaya ma suna buƙatar haka.

A shekara ta 2007, ayyukan ƙwarewa da dama sun faru : an tafiyar da ayyukan tattalin arziki, da bisa littafin karin maganganu na Arewa, da bunƙasa aikin kaɗa.

A shekara ta 2008, ayyukan ƙwarewa 11 suka faru :

  • bmasu aikin gyaran jiyoyi 3 waɗanda suka yi aiki a babbar likitar Yamai,
  • malaman kiwon lafiya 2 a babbar likitar Dogon Dutsi,
  • mata 2 waɗanda suka yi wani baza-koli mai laƙanin «zaman yarinta a Nijar, ko « être jeune au Niger » a faransance,
  • da ɗalibi 1mai ilimin zanen siffar gini,
  • da ɗalibi 1 wanda ya bi sau-da-ƙafa makarantun da ke karɓar yaran da suka wuce shekarun shiga makaranta,
  • ɗalibai 2 sun yi aiki don inganta tsarin ayyukan Tarbiyya Tatali a Faransa da Nijar, da kuma tsarin tattalin al’adun Arewa.

Akwai wani jagoran da aka rubuta dangance da littafin da Marine Rétif ta yi a shekara ta 2007, inda za ku samun amsoshin wasu tambayoyinku.

Shekarar 2010 Hulɗa tsakanin Afirika da INSA

Kowace shekara wannan ƙungiyar ta ɗalibai injiniyoyi na jami’ar garin Rennes tana aiwatar da wani aiki a Afirika. Aikin da suka shirya a shekara ta 2010, shi ne samar da tsarkakkun ruwan sha a Ɗankatsari ta hanyarhulɗa tskanin Ɗankatsarin da Cesson-Sévigne. Ɗalibai injiniyoyi ko ɗaliban jami’a, su 13 za su yi aikin wata 1 da rabi a Ɗankatsari.

A shekara ta 2010, mutum 20 aka sa ran za su yi ziyarar zumunci a Nijar tare da Tarbiyya Tatali.

A shekarar 2011, bala’in da ya samu ya sa muka soƙe ziyarun cuɗayyar juna

Farkon 2011 Sakamakon kamawarsu a wani lafiyayyen gidan cin abinci a birnin Niamey, da kuma ɗanye rasuwar Antoine de Léocour da abokinsa Vincent Delory,da kuma rasuwar soja uku na ƙasar Nijar, Abubacar Amankaye, Abdallah Abubacar, da Abdu Alfari, da suke ƙokarin ceto su ya sa muka soƙe muna fatan na ɗan lokaci shirye shiryen mu na cuɗayyar juna.
Lokacin da aka kama shi, Antoine na Nijar ne a zaman kansa. Ziyarar shi ta farko a ƙasar Nijar ya yi ta ne lokacin bazara a shekara 2008, a matsayin ɗan kwas, ya yi aiki bisa hurojen na kayan al’adun Arewa musamman ma bisa shaidun tsofin ɗaliban makarantar .

Stagiaires 2007 au Niger
2007