Littafi ne mai taƙaitaccen shafi 60 da RAEDD ta yi tare da taimakon kudi na Birnin Rennes da AECIN.

Abinda ke ciki shi ne kamar haka:

  • Daga yarinta har girma ; Mene ne balaga? Balagar ‘yan samari. Balagar ’yan mata.
  • Yaya ake kiwon lafiya : Mene ne tsabta? Tsabtar jiki. Tsabtar gida. Abinci mai kyau da tsabta.
  • Haɗin kai: Mene ne ƙauna?
  • Haifuwa : haifuwa, mene ne? Lokatai na juna biyu. Haihuwa.
  • Tsarin iyali, mene ne? Zaman juna biyu ba cikin an so ba
  • Hakkin yara. Auren yara ƙanana.

An yi wannan rubutun bayan samun shawarwari da dama. Babban muhimmancin na edita, da na marubuci da kuma mai yin zane, duk ’yan Nijar, ya sa an samu daceccen littafi mai bayyana cikin sarari a shirinsa, muhimmancin shirye-shiryen iyali musamman wajen yaƙin auren kananan ‘yan mata (Kamar yadda gwamnatin Nijar take yi).

An samu halartar mutane 21 wajen horo da aka yi game da amfani da littafin, maza 11 da mata 10, mallaman kwalejin Matankari da Ɗankatsari da masu kulawa da tsarin iyali wadanda ke yawo cikin kauyuka da garuruwan Dankatsari da Dogon Dutsi a watan Disamba 2017. Mace da namiji ne suka gudanar da horon. Mahalartan sun ba da shawarar a fadada littafin tare da buga shi cikin harsuna Nijar, (Hausa na yankin). Ya nuna kyakkyawan yardar malaman makaranta, maza da mata da masu tsarawar iyali da abubuwan da ke cikinsa. Wannan littafin yana dauke da amfani don samun horo da bayani. Ya ba da damar samun lokaci na yin tattaunawa, a ciki har da bukatar malaman na zamansu marasa zargi tare da ‘yan makaranta.

Taron na biyu na mutane 24 ya faru a watan Yuni 2018, ya shafi dukan malaman makarantar kwaleji masu koyar da kimiyyar rayuwa da ta Duniya na garuruwan Ɗankatsari da Dogon Dutsi, maza ashirin da biyu da mata biyu.

Horar da yadda ake amfani da karamin littafin da aka tsara a karshen 2020 a Dankatsari ya jinkirta saboda hana ayyukan horo da gwamnatin Nijar ta yi saboda COVID. A ƙarshe ya faru daga 12 zuwa 14 ga Maris, 2021. Masu horarwar su ne Géneviève Courjan da Mahamadu Roro, membobi biyu na ƙungiyar rubutun ƙasidar, waɗanda suka zo daga Yamai. An tsara shi ne don horar da mutane 30 (mata 15 da maza 15). A ƙarshe, an horar da mata 14 da maza 16. Sababbin littattafai ɗari shida na ƙasidar aka buga kuma aka rarraba su ga waɗanda ake horarwa.

Damar zuwa ga dukan labaran nan. Littafin yana cikin fim din “Yan mata uku a Dankatsari” kuma ana amafani da shi wurin koyarwar ilimi game da ba da bayani bisa abin da ake nufi da auren kananan ‘yan mata.

Illustration de la page de couverture