Guri da matakan aiki
Gurin wannan tsarin « na ƙaramar hukuma dagane da ci gaban garuruwan ƙauyen Dankatsari gaba ɗaya na Nijar » shi ne ƙarfafa ayyuka jihar Dankatsari cikin fannonin dayawa.,
- Shirya dubarun samun ruwa
- Kara ƙarfafa tallahi zuwa ga ma’aikatunan magajin gari (don kulawa da takardun haihuwa, karƃar kuɗin haraji, ci gaba da tafiyar da wuraren ajiyar abinci, da kuma injin nikan hatsi).
- Girka tsarin na noma da kiwo.
- Horon mata.
Wannan tsarin ya shafi bangarori uku
- Gundumar Dankassari da ke yin tsarin ayyukanta, kuma ta yi su tare da taimokon ‘yan hulɗarta, tare da kokarin magajin garin ko da yaushe.
- Ma’aikatar shirya dubarun samun ruwa na Dogonduci da RAIL (Rukoma ta taimokon ayyukan jiha) masu yin nazarori.
- Kwamitin kula da harakokin gari masu ci gaba da ayyuka.
Abokan hulɗa na shirin
Gudumar Cesson-Sevigne da Dankatsari, Gwamnatin Nijar, Ma’aikata mai kula da harakokin waje, Jihar Bretagne, Ma’aikatar ruwa ta Loire Bretagne, SMPBR.
Ayyukan da aka yi a 2015-2016
Na 1 – Aiwatarda tsarin samun ruwa
Na 2 – Ingantarda ayyuka ma’aikatar magajin gari
Aikin jan hankalin jama’a da ‘yan majalisa, da shugabannin gari bisa karɓar kuɗin haraji da ta ci gaba.
Bayan kilga abinci na dukan bankunan hatsi da injin niƙan hatsi na garin, an yi horon COGES na bankunan hatsi da na injin niƙan hatsi da kuma kayan aikin niƙa. An gyara bankunan hatsi biyu, an kuma canjawa guda wuri. An kuma kafa guda. An kafa injin nikan hatsi biyu an gyara kuma uku.
Na 3 - Horon mahalli, dasa itatuwa
An yi nazarin binciken bisa aikin lambu da kiwo. Wadannan nazarorin su ba ma’aikatar magajin garin Dankatsari damar sanin bukatu da abubuwan da ya kamata na ma’aikatar da jawo hankalin abokan aiki.
Na 4 – Horon mata
Horon mata a cikin wani mataki shiri ne na muhimmanci domin yana samar da ilimi ga ’yan mata sa’anan kuma ya sa mata su samu incinsu wajen biya wa kansu bukatunsu.
A 2015 tsarin ya biya kuɗin yaki da yahilci na kungiyoyin mata biyu, da kayan aikin ungozuman wato amalanke. Kayan amalanken na ƙara masu albashi.