Al’umma, masamman ma mata sun amince wa ungazumai masu kula da su a lokacin haifuwa. Yawancin ungozuman ba su samu horon komi ba kan wannan aiki .

Shi ya sa horar da su yake a sahun gaba a fannin kiwon lafiya

A ƙasar Nijar, akwai babbar matsala a fuskar kiwon lafiyar mata da yara, inda matan da yawa ne suke rasuwa wajen haifuwa.

Binciken da muka ƙaddamar a ɗakunan shan magani na ‘’dapartaman’’ Dogon Dutsi, ya nuna cewa horar da ungozumai, abu ne mai mahimmanci a wajen malaman likita, da wajen al’umma baki ɗaya.

Gurin bayar da horon

Wannan horon zai taimakawa wajen kokowar shawo kan matsalar mace-macen mata da yarirai, tunda ungozuman za su iya gano ciki mai hatsari da haifuwar da ba ta zo daidai ba.
Bayan haka, horon da suka samu bisa riga-kafin haifuwa, zai sanya su nuna ma mata hanyoyin zamani na tsakaita haifuwa.

Tsarin ayyukan horarwar

An shirya zaman taron horarwar na sati 2 a Dogon Duci. A karshen wannan horon kowacce ungozuma za ta samu jaka cike da kayan aiki (karamin sanduki, tawul, fitilar ƙwai, fitilar hannu, kayan ɗunki, sahani, tabarma, bokiti, leda) da kuma wasu kaya kamar su (safar hannu, reza, zare, sabili, magunguna iri iri, da kaɗa da sauransu).

Ungozumai 73 ne aka yi wa horo daga shekarar 2008 zuwa shekarar 2013.

2008-2013

A shekara ta 2008, ungozumai 12 na kwamin ta Dankatsari muka ba horo, mun yi wannan aikin ne tare da taimakon ƙungiyar ‘’Fredie la vie au Niger’’. http://www.fredielavieauniger.org/]".

A shekara ta 2009-2010, ungozumai 20 aka ba horo : 10 na kwamin ta ’Dankatsari dangance da hulɗar tsakanin ‘’Cesson- ’Dankatsari’’, 10 a cikin garuruwan karkara na kwamin ta Dogon Duci ta hanyar wani sabon taimako daga ƙungiyar ‘’Fredie la vie au Niger’’.

A farkon 2011, sabin ungozumai 16 aka ba horo game da hulɗar garin Rennes, daga kwamin ɗin Sukukutan da Dogonkiria suke.

Farkon 2012, sabin ungozumai 25 suka samu horo game da hulɗar garin Rennes da ƙungiyar ‘’Fredie la vie au Niger’. Daga kwamin na CSI ɗin Dankasari, Arewancin Dogon Dutsi, Dumega, Guecheme, Kieche, Kore Mai Ruwa, Lido, Matankari, Cibiri.

Sakamakon wannan horon dai na ungozumai yana cikin littafinmu na “Da da rai a Nijar” wanda aka wallafa ran 13 ga watan Mayu 2012.

Wadansu daga cikin ungozuman nan sun samu amalanke na shanu, saboda tafiya likita da gaugawa in a samu aifuwar da ta zo da gardama, an yi shi ne da taimakon hulɗar tsakanin ‘’Cesson- ’Dankatsari’’.

An yi wa ungozoman 10 na Dankatsari horo na kwanaki goma sha biyar a watan Disamba na 2017 da kuma wani, har ila yau, ga ungozomai goma na Dankatsari, a watan Yulin 2020. Kuma an ba ungozoman nan 20 kayan aiki.

An horar da sabbin ugozomai 20 a Dankatsari, a watan Oktoba 2021 da Yuli 2022. Sun nemi a saka musu rigar aiki wato uniform mai launin kala.

Samarda shanu da tarko

Wadansu daga cikin ungozuman nan sun samu amalanke na shanu, saboda tafiya likita da gaugawa in a samu aifuwar da ta zo da gardama, an yi shi ne da taimakon hulɗar tsakanin ‘’Cesson- ’Dankatsari’’. -> 500].

Ta haka ne aka samarwa ungozomai talatin da tara kayan aiki daga shekara ta 2011 zuwa 2020 (akasarinsu game da kudin da suka biya na amalanken su).

Formation des matrones, 2008
2008