Ranar 13 ga watan mayu, ranar sallar matan Nijar

Ranar 13 ga watan mayu 1991, matan Nijar sun yi Allawaddai ga wata mummunar wariya da aka yi masu a lokacin kafa kwamitin ƙasa na shirya babban taron ƙasa, inda aka ɗauki mace ɗaya (1) tal cikin mambobi 40 na kwamitin; sanin kowa ne kuma da mata ne kashi 52 cikin 100 na al’ummar Nijar. Ran nan, matan Nijar na kowane irin matsayi suka yi jerin gwano don nuna baƙin cikinsu har zuwa ma’aikatar Ministan harakokin waje inda kwamitin yake zaman taron nashi. Sai da suka ciyo nasara tunda an ɗaga yawan matan daga 1 zuwa 5 ; bayan haka, gwamnati ta ɗaukaka wannan ranar ta 13 ga watan Mayu, ranar salla ce ta matan Nijar baki ɗaya.

Taimaka wa matan Nijar

Tun shekara ta 2005 Tarbiyya Tatali take halartar wannan sallar ta 13 ga watan mayu inda take yaɗa bayanai daga wata ƙasida bisa matan Nijar da ayyukan da suke zartawa.

Ta haka ne aka wallafa ƙasidu kamar haka :

  • a shekarar 2005 « Matan Arewa : Sarauniyar Lugu »;
  • a shekarar 2006 « ƙasida bisa matan Nijar masu cikakkar niyyar ayyukan ci-gaba mai ɗorewa»;
  • a shekarar 2007 « ɗiyan matan da suka gaji halin Sarauniya : halin nagari tamatan Nijar »;
  • a shekarar 2008 « ƙasida mai zancen amfanin tsakaita haifuwa » ;
  • a shekarar 2009 « ƙasida mai zance bisa auren latse » ;
  • a shekarar 2010 « ƙasida mai zancen makarantar ‘yan mata » ;
  • a shekarar 2011 “Les femmes nigériennes prennent leur place dans la vie publique”,
  • a shekarar 2012 “Ba da rai a Nijar”
  • a shekarar 2013 “Ruwa falala Lugu !”
  • a shekarar 2014 “Cin nassarar karatu don samun moriyar rayuwar gaba : kokoyar matan Nijar.”

A ranar 13 ga watan mayu ta 2007, Tarbiyya Tatali ta kawo taimakonta wajen tsarin wata gagarumar salla a garin Lugu.

Mujallar Tarbiyya Tatali

Tun shekara ta 2015, Tarbiyya Tatali na yin taron nurma ta ranar mata a Nijar tare da bugawar mujallarta a ranar 13 ga watan mayu.

Bikin yanki a Lugu a 2023
 
An yi bikin ranar 13 ga Mayu da daukacin yankin Dosso a Lugu , bayan rasuwar Sarauniya Aljimma da nadin Sarauniya Kambari a farkon 2023. Taken bikin na bana shi ne ’Mata da Ci Gaba ’ . bukatar magajin garin Dankatsari ya bukaci, kungiyar AESCD ta bada gudunmuwa ta hanyar daukar nauyin ziyarar dalibai 100 da suka fito daga kauyukan karamar hukumar Dankatsari . Sun kwana a nan, sun koyi tarihin ƙauyen kuma sun halarci wani fim na CulturePlus , reshen al’adu na Nuvel Espoir.

Brochure 13 mai 2011