Tarbiyya Tatali, mamba ce ta haɗin gwiwar ƙungiyoyin mata na Nijar cewa da CONGAFEN wadda aka haƙiƙanta zamanta tun 1995. Gurin farko da CONGAFEN ta sanya gaba shi ne ta ba sauran ƙungiyoyin farar hula damar haɗa kansu don gudanar da ayyukan kyautata jin daɗin rayuwar matan Nijar.