Bankunan cimaka na garuruwa

A cikin kowane gari, wata ma’ajiya ce ake keɓewa don kimshe rabin cimakar da aka sumu a dalilin wasu kud’i da ƙungiyar take badawa. A hannu manoma ake sayo cimakar a ‘’farashin’’ kasuwa, kuma in lokacin ƙarancin cimakar ya zo, sai bankin ta sayar masu da wani ‘’farashin’’ da ya zarce na sayowar. Da wad’annan kudin ne ake sake cika bankunan, har ma a bunƙasa su in lokaci ya kewaye. Ribar da ake samu,a hannun mutanen garin take, maimakon ta amfani manyan ƴan kasuwa kamar yadda abin yake wakana a can baya.

An kafa bankin cimaka d’aya a garin Lugu, da wasu 4 a garin ‘’ Gawuna’’ da Guezanaya’’ (AECIN) “Anguwal Saulo da Goofat” (Aminnan Nijar) da ke arewacin yakin a skekara ta 2006.

A shekara ta 2010, bankin cimaka 2 aka kafa a garin Kujak da Daɗin kowa a cikin kwamin ta Ɗankatsari ta hanyar wani taimako daga birnin ‘’Cesson’’

Idan ana son bankin cimaka ta bunƙasa ba tare da tallafi daga waje ba, sai an kafa warni kwamiti wanda za ya riƙa kulawa sosai da ayyukan tattali. Ƙungriyar ‘’RAEDD’’ za ta kulawa da horar da mambobin kwamitin.

A shekara ta 2016, bayan nazarin bankunan hatsi da injinoni, an yi wani shiri na horon illahirin kwamitocin bankunan hatsi na jihar Dankatsari. An gyara bankunan hatsi na Kujak da Dadin Koua, na garin Lugu mai kamar aiki biyu an sake mashi wuri zuwa Faya an kuma kafa wani sabon bankin hatsi a Duzu.

An samu damar gyra da kyautata bankunan hatsi na Gauna da Guézanaya (na jihar Matankari) tare da goyan bayan AECIN an kuma kafa kwamitocin masu kulawa da su.

A shekarar 2021, an kafa bankunan hatsi a Garin Agur, da kuma Kumtchi a cikin karamar hukumar Dankatsari. Duk bankunan hatsi sun sami horo don COGES ɗin su kuma RAEDD ta dauki nauyin kulawarsu ta yau da kullun.

A farkon shekarar 2022, an gano wasu kauyuka uku a cikin karamar hukumar Dankatsari musamman wadanda ke fama da rashin abinci a lokacin noma na 2021, don kafa masu sabbin bankunan hatsi; Waɗannan ƙauyuka su ne na Angual Kassa, Lillato da Nakigaza Dechi, masu yawan jama’a 3000. Taron ya ba da damar samar da kudade ga bankunan hatsi na Angual Kassa da Lillato. Kauyuka hudu a cikin karamar hukumar Dogonduchi suma sun amfana da sayan buhunan hatsi ga bankunan hatsi. Waɗannan su ne Gauna, Guezangna, Dume da Baringo.

Réserve de mil