A ƙarshen horo na kwanaki 3 na farko akan tsarin iyali (haɗi tare da labarin 357), maza da mata gaba ɗaya sun bayyana burinsu na fa’ida daga sake nazarin horon don tuna abubuwan da suka gabata da gabatar da kuma sabbin abubuwa. Sun kuma yi fatan samun kayan aikin da za su taimaka musu wajen isar da sakonnin su.

Wannan shi ne ya sa AECIN da AESCD suka gabatar da shawarwari game da aiki da hotuna, wadanda RAEDD ta inganta, kuma suka ci gaba da samar da su domin su damka su ga ragowar al’umma a karshen horon su.

Manufar ita ce a fassara manyan sakwanni 5 da Tarbiyya Tatali ta bayyana kan mahimmancin sarrafa yawan haihuwa (ba wai tazarar haihuwa ba kawai har ma da kula da yawan iyali), wanda mutanen da aka hora za su yada ga mazauna kauyukan:

  • mahimmancin haihuwa ba hadari: hanyoyin hana daukar ciki na zamani da tazarar haihuwa suna inganta lafiyar uwaye da yara da kuma yanayin rayuwar dangi,
  • kin yin aure da wuri kafin shekaru 18 yana hana haihuwa wajen kananan mata hakan zai dace da lafiyar su da ta ‘ya‘ yan su, wannan na saukaka karatun yara mata.
  • mahimmancin kulawa da yara a cikin al’amuran motsin rai da na abinci: yana da kyau a sami ‘ya ‘ya kaida kuma a kula da su sosai,
  • makomar yara ta fi kyau idan ba su da yawa, iyali da ya fi dacewa shi ne wanda iyaye za su kula da yaransu kan lamuran lafiya, ilimi, abinci, da sauransu ba da wuya ba.
  • karfafa karfin mata ta hanyar aikin yi don samun kuɗin ya fi sauƙi idan ba su da yara da yawa.

AECIN da AESCD sun nemi zane-zane mafi dacewa, musamman ta takardu da yawa da aka jera da / ko kuma aka tsara na Tarbiyya Tatali: nazari game da “ilimin mutum da na zamantakewar mu”, ƙasidar nan ta “Lafiyata da ’yancina na matashi” (haɗi tare da labarin 414), daftarin aiki daga ANBEF, CEDEF (haɗi da labarin 129), da sabon zane wanda yake wakiltar majalisar birni tare da mata da maza.

A karshe, takardun zane-zane guda 27 ke kwatanta manyan surorin da aka tattauna yayin zaman horo, tare da fassarar rubutun da Hausa:

An riga an gwada su bisa aiki na kula da tsare tsare a Bawada-Dagi (Dankatsari), Batanbéri (ƙwamun ta Dutchi), Montéré da Mailo, (tare da mai ɗaukar hoto Aziz don ɗaukar hoto kan amfani da sabbin abubuwan aiki na mata masu ba da horo da kuma mai gudanarwa Maimuna Kadi).
An kuma yi amfani da su yayin horon “sake maimaita horo” na mata 60 na farko da aka horar a Dankatsari a cikin 2018, kuma aka ba su kayan aikin a ƙarshen maimaita horon don su yi amfani da su.