Tsari takwason likita a Nijar

Ba a dace da samun hanyoyin gudanar da tsarin takwaso a cikin ƙasar Nijar ba. Akwai wuri shara da takwaso da yawa a cikin birane da ƙauyen Nijar.

A cikin manyan asibitocin kasar kadai ake ware takwason gidan likita. Cibiyoyin Kiwon Lafiya masu sunan (CSI) ba su da wurin toye shara. Suna da rami don ƙona su, amma suna fama da rashin anfani da horo na ma’aikata. Ba’a da kayan da ake bukata don ware kayan sharar asibitocin. Wannan yana ƙara sa kamuwa da cututtuka da dama kamar na jima’i (MST da IST).

Tsarin

Wannan aikin ya biyo bayan ƙaddamaware kayan aiki na likitocin da ke da alhakin ƙananan hukumomi. Likitocin masu aiki da RAEDD ne suke bukatar samun maganin wannan matsalar.
Shirin na nufin rage kamuwar cututtuka kamar na MST ko IST a cikin Cibiyoyin Kiwon Lafiya (CSI) 26 na Department ɗin Dogondutsi da Tibiri.
Wadannan ma’aikatan CSI guda 26 za su kasance da kayan aikin na sanya sharar gida na musamman da aka kera a Dogondutsi kuma za a horar da ma’aikatan kula da su don tsabtace lafiya da maganin cututtukan kiwon lafiya, wanda zai taimakawa wajen shigar da tsarin sharar gidaje da ke hade da kulawa da toyewar su. Kowace CSI za ta amfani da abun sa takwaso guda biyu da amalanke guda, wanda masu sana’a na Dogondutsi suka yi, da kuma horor da ma’aikata biyu masu kulawa da tsabtar wurin.

Kwarewar da aka samu da kuma horar na iya zama tushen horon juna a yanki da kuma a cikin kasar gaba daya.

Wannan aikin dai ana yin sa ne da tallafawar birnin Rennes da departement na Ille et Vilaine da kuma kudaden da AECIN ke bayarwa.
An kammala kayan aikin CSI guda 26 kuma an gudanar da horon ma’aikatan a farkon shekarar 2018.