An kammala wannan mataki.

A lokacin da Tarbiyya Tatali ta ƙulla da garin Lugu a shekara ta 2002, makarantar tana da matsaloli, har ma anso rufe ta, tunda yara 20 ne kawai suke zuwa kai-da-kai.

Taimakon da makarantar ta samu

Abin da aka yi a shekara ta 2002, shi ne bai wa yara abincin rana ; yawanci sun zo daga garuruwan kewaye. An ci nasarar yin haka tunda yara 55 suke zowa makaranta kowace rana, inda suke samun abinci na hatsi, da shinkafa, da wake, da kuma nama a wani lokaci. Mutanen garin ne suka sayo abincin ta hanyar wani tallafi daga ƙungiyar AECIN, kuma su sukaɗauki nauyin albashin macen da take daka ma yaran hatsi.
Garin ya samu hamzarinɗaukar nauyin abincin tun daga shekarar 2004 zuwa 2005, kuma yawan yaran bai rage ba. A halin yanzu, aji 3 makarantar ta ƙumsa (na1 ; na3 ; da na 6).
Ta hanyar tallafin da tsarin taimaka wa yaƙi da talauci na ƙasar Kanada yake kawowa, Tarbiyya Tatali ta kawo wa makarantar littafai da wasu kayan aikin koyarwa waɗanda aka damƙa a hannun kwamitin tattali.

Tsarin yaƙi da jahilcin mata

A shekara ta 2006-2007, an gudanar da yaƙi da jahilci na wani rukunin mata a garin. Matan sun nuna niyyarsu kuma sun riƙa halarta sosai.

Passion d’apprendre
{{}}