An kammala wannan mataki.

Cibiyar ba da horo kan ayyukan ci-gaban al’umma « C.F.D.C »

Gwamnatin Nijar ta kafa irin waɗanga wuraren horon tun shekara ta 1996 domin rage zaman banza, da yawan tafiya cin rani, da kuma kyautata rayuwar ‘yan ƙasa ta hanyar horarwa kan fannin koyon sana’o’i da fusa’o’in noma.
Saboda haka, har wani diriktar gwamnati ta naɗa ; sai dai a zuwansa wurin, ko ofushin babu, balle kayan aikin.
Da taimakon « RAEDD », da kuma ban hannun « GREFF » a fannin ba da horo, cibiyar “ C.F.D.C” ta Dogon Dutsi ta fara gudanar da ayyukan a lokacin zafi na shekara ta 2003. Cibiyar « C.F.D.C » ta kama ƙarfi tun lokacin da kwamin ta Dogon Dutsi ta ba da hili inda aka gina wurin bai wa matasa horo ; tun wannan lokacin , ƙungiyar ta ba da horo a fannoni daban daban, kamar : ayyukan ƙarfe, da tsarin wayoyin lantarki cikin gini, da gyare-gyaren pampuna, da ɗinki, da dahe-dahe, da wasu fusa’o’i da ilimin kyautata rayuwar yara ƙanana, da kuma yaƙi-da-jahilci.
Wuraren horo na C.F.D.C suna taimaka wa cibiyoyin ayyukan ci-gaban kwaminoni, waɗanda magadan gari na kwaminonin karkara na dapartama ta Dogon Dutsi suka nemi kafawarsu a shekara ta 2006. Tun lokacin nan ne malaman waɗannan cibiyoyin suka samu horo kan aikin koyarwa da fusa’o’i, tare da goyon bayan ƙungiyar « Swisscontact Niger », da kuma « GREFF ».

Cibiyoyin ayyukan ci-gaban kwaminoni « C.D.C »

Gurin waɗannan cibiyoyin shi ne na horar da matasa waɗanda ba su yi boko ba, na kwaminoni 9 da suke cikin yankin. Horon da ya dace wa kwamin ɗinsu a fannin noma da sana’o’in hannu.

A cikin kowace kwamin, an gina cibiyoyin « C.D.C » ; sai dai a riƙa kyautata tsare-tsarensu.

Gurorin hurojen su ne:

  • Bai wa matasa horo a cikin kowace kwamin ;
  • Shirya tarurrukan ƙarin ilimi a fannin (yaƙi-da-jahilci, da fusa’o’i daban daban, da iya tsara ayyuka da tattali) saboda malaman cibiyoyin ;
  • Faɗaɗa cibiyoyin da inganta su, da samar da kayan aiki;
  • Horon kwamitocin kwaminoni masu shugabancin cibiyoyin

Ayyukan horon da aka tanada, sun shafi masamman fannin noma ( kayan aiki kamar, na lambu, da noman sabbin abubuwa da suka shigo).

Ta hanyar tsarin AECIN na keken hawa 500 da aka tattaro a ƙasar faransa a shekara ta 2007, kuma aka raba wa makarantun “kwaleji” na yankin Dogon Dutsi. Wannan ya sa aka samu damar shirya horo daban daban na farko a fannin gyare-gyare, wato “makanike”

Hurojen yana ƙarƙashin shugabancin wani kwamiti wanda ya haɗa magadan gari, da haɗin gwiwar ƙungiyoyin ci-gaban yankin. ƙungiyar RAEDD ce take jagorancin kwamitin, tare da goyon bayan « GREFF » da « AECIN » da wasu abokan hulɗa daban. 

Diplomes au CDC