A shekarar 2014, ran 13 ga watan mayu, Tabiyya Tatali ta yi wani ɗ an littafi bisa « ci gaba ta karatu don cin ma gurin gobe : Kokowar ƴan matan Nijar ». Mun lura da ‘yan mata dayawa da suka bar makaranta don aure sun komo kwaleji, to su ne muke so mu taimaka wa.

Haka ta samu ne a Dogondutsi don taimaka wa kananan matan nan.

  • RAEDD za ta samo maza da mata masu taimakawa da biyan kuɗin makarantar.
  • Taimakon AECIN don sayen littattafai da wasu kayan makaranta.

Mata 42 ne suka samu taimako a shekara 2014_2015. A watan july 2015, a cikinsu 18 ne suka samu jarabawa ta BEPC.

Sai dai a kara da cewa kuɗin wannan taimako kamar 2/3 na shigowa daga cikin kasar Nijar.

A 2015-2016, an gudanar da aikin wurin mata talatin na yankunan karkara Matankari. A rashi kwalejin mai zaman kanta a cikin wannan kwamin, dole aka gina aji kuma aka kawo kayan aiki da tabbatar da samun malaman masu koyarwa. An samu yi wannan tsarin ne tare da taimakon kuɗaɗe da jama’ar jihar Matankari suka kawo, da na AECIN.

Rishin samun nasara sosai a BEPC a shekara ta 2016 a matakin ƙasar duka ya yi tasiri ga sakamakon : uku kawai suka samu. Amma matan sun na ta ci gaba kuma sun yi niyyar ba da himma ga horo don samun nasara ga jarabawa ta 2017, tare da goyon bayan ’yan jihar Matankari da AECIN.

A shekara ta 2016-2017, mata 20 suka yi jarabawa ta BEPC a Matankari,biyu kawai suka ci jarabawar.