An kammala wannan mataki.

Teburorin karɓar haifuwa

A shekara ta 2004, ƙungiyar taimakon juna ta ƙasa cewa da ‘’Association’’ de solidarité internationale’’ ta jami’ar ‘’santander’’ (ƙasar spana) ta wadatar da garin Anguwal Saulo da teburorin karɓar haifuwa. Nan gaba duk wata haifuwa a garin, a ɗakin kiwon lafiya ake yin ta.

Na’urorin ruwan zafi masu aiki da zafin rana

A shekara ta 2005, an sayi na’urorin ruwan zafi 2 masu aiki da zafin rana don amfanin gidajen likitar haifuwar Dogon Dutsi da Matankari, ta hanyar taimakon ‘’santander’’. Kenan, an sulhunta aikin matan da ke zowa daga gida suna ɗora ruwan zafi a gidajen likitar ; nan gaba masu biƙi da jariransu za riƙa yin amfani da ruwan zafin waɗannan na ‘urorin.
Haka kuma, ta hanyar wannan taimakon na ‘’santander’’, gidajen likitar haifuwar Birnin Lokoyo da na Dogon ƙirya sun samu na’urorin ruwan zafin.

A fannin gadajen jarirai da matalu

A shekara ta 2006, gidan haifuwar Dogon Dutsi ta samu taimakon gadajen kwancin jarirai da matalunsu daga ‘’Lise’’ na ‘’Saint-Martin’’, waɗanda ƴan makarantar ‘’CFDC’’ suka ƙera a nan take-yanke.
A shekara ta 2008, an sayo sabin matalu 20 don canjin waɗanda suka lalace a gidan haifuwar babbar likitar Dogon Dutsi.

Chauffe-eau solaire
{{}}