An kammala wannan mataki.

Bayan shawarwari da yawa, da kuma wani tallafi na masamman da aka samu, a shekara ta 2004 Tarbiyya Tatali ta yi niyyar ɗaukar wata babbar malamar likita don aikin ƙaramar likitar Dogon Dutsi, kuma ta riƙa biyan ta albashinta.

Dakta Seiyaba

A Dogon Dutsi ta ke kuma ita ce shugaban hurojen mu « Lafiyar mata da yara » daga shekara 2004 zuwa 2011.

A shekarar 2004 ƙungiyar hulɗa ta duniya ta jami’ar Santander (Spain) ta taimaka wa fofishinta a gidan lafiya (iyakwandishan, frigidaire).
An ɗauke ta aikin gwamnatin Nijar watan september 2005.

Daga watan mayu 2008 ta zama shugabar likitan Dogon Dutsi kuma mataimakiyar likita ta gundumar kiyon lafiyar Dogon Dutsi.

Daga october 2011 ta samu wani horo na wata 21 a Burkina Faso bisa yawan jama’a da lafiyarsu.

Docteur Seiyaba

Dokta Aissa

Sabuwar Dokta mai zaman kashe-wando, da Dokta Seiyaba ta hadu da ita lokacin da take kwas a likitar Dogon Dutsi, RAEDD ta ɗauke ta aiki a watan december 2010 tare da taimakon AECIN da Fredie rayuwa a Nijar. Likitocin Dogon Dutsi aikin mulki ya ke sa ba su samun damar saduwa da maras lafiya.

Tun october 2011 ta zama shugaban hurojen « lafiyar mata da yara »

Ta zama cikakkiyar ma’aikaciya ta gwamnati a watan mayu 2012.

Ta bar Dogon Dutsi a shekarar 2017.

Docteur Aissa