AECIN ta yi tsare tsare, tare da sauran ƙungiyoyin duniya (Gidan Jafananci, gidan sana’o’i na duniya, GREF) da kuma ta hanyar hada kai na kasa ta duniya ta Rennes, wuraren nazari a makarantu a shekarar 2014-2015, da kuma a farkon shekara 2015-2016 a makarantar Leon Grimault ta Rennes.

Makarantar Leon Grimault, na aiki da dabaru na Freinet, mai suna Freinet malamin makaranta ne a cikin farkon karni na ashirin. Koyawar dai ta dogara ne bisa hanyar halittar yaro.

Kera zane zane, hadin gwiwa da kuma samun inci, su ne a cibiyar ilmantarwa.

Wurin nazarin (awa ​​daya a mako a tsayon makonni goma ) ya sa mahalartar nazarin –kamar su goma ko wane lokaci –gani cikin tsare tsare ban shawa, da sauransu, Nijar , da al’adunsa da kuma salon da mazaunanta suke ciki.
A karshen shekarar 2015, yara na TAP (lokacin nazari a makarantu ) su gudanar da wani nuni bisa kasashen daban-daban da “suka ziyarci” a lokacin tsawon koyansu na wata uku.