An kammala wannan mataki.

Yin zare da saƙa

Wannan aikin na matan garin Lugu, ya samu tallafi daga tsarin da ƴawa na ƙanana basussuka tun shekara ta 2003, ta hanyar sayen kaɗa da bada bashi domin kafa ƴan ƙungiyoyin masu saƙa, da bada bashi domin tara yadudukkan da za a sayar a cikin kasuwanni.

Gurinmu shi ne na sake farfaɗo da aikin da jama’ar Lugu suka saba, na yin zare da saƙa, don tallafa ma mata. A halin yanzu, ba kamar can da ba, ƙarancin ruwan sama ba ya bada damar fitowar kaɗa.
Kaɗa zare yanaɗaya daga cikin ayyukan gargajiya na Sarauniya. Amma a garin Lugu, kaɗan ne tsofin matan da suka riƙe yin wannan aikin; sai Sarauniyar da kanta. A cikin shawarwari tare da mutanen garin ne aka fara kawo zancen taimaka ma matan don su farfaɗo da aikin zare da bunƙasa saƙa. Hakan zai sanya su riƙe wanga tsofon aikin nasu, har ma su koyi sabbin fusa’o’i, kuma su riƙa samun ƴan kuɗi.

Sake farfaɗo aikin zare da saƙa

Tarbiyya Tatali ta shawarta ma mata su kafa ƴan ƙungiyoyi. Ta haka ne aka ne aka girka ƙungiya 5 masu ƙumshe da mace 6, kowacce ; kowace unguwa tana da ƙungiyarta.
A shekara ta 2003, mun saya ma garin kaɗa ta jika 100. ƴan makaranta ne suka fitar da ƙwayoyin kaɗar, suka shace ta san nan mata suka yi kaɗin zaren. A ƙarshe sai masaƙa maza suka yi saƙar kamar yadda aka sani a gargajiya. Ana gudanar da aikin zare sosai a garin Lugu, har ma cikin wasu garuruwa inda ke da mata mambobin ƙungiyoyin.
A sayar da bandir da yawa na yadi a Dogon Dutsi, da Yamai, da Rennes da kuma Dakar. Ana yin abubuwa da yawa da kaɗar garin Lugu, kamar barguna, da dararuwa, da kayan jiki,da kayan jarirai, da na bori, da na sanya layu. An biya bashin farko da ƙungiyar ta bayar, kuma an sayi kaɗa mafi yawa don aikin shekara ta biyu.
Sarauniya ta fitar da zarenta na kanta a shekara ta 2004 ; abu ne wanda ba a saba gani ba. Dukan mata sun halarci sabgar wadari inda ake warware zaren, a kewaye garin don a ji daɗin saƙar.
Amma bayan an yi isasshen zare da kaɗar, sai matan suka yi lura da maza masaƙa ba su da yawa, kuma sun tsufa. Sai suke cewa : « Muna iya yin fiye da haka ; amma masaƙi guda kaɗai ne cikin garin » ; sun so a ce kowace ƙungiya tana da masaƙi. A ƙarshe, kuɗi kaɗan matan suke samu tunda babu masaƙa. Wannan matsalar ta jawo shawarwari da yawa cikin al’ummar garin.

Idan matan suka shiga yin saƙa

Shawarar mata su shiga yin saƙa ta fara fitowa, ko da yake ba a taɓa gani ba. A wasu yankunan ƙasar Nijar, saƙa aiki ne na waɗanda suka yi gadon shi kaɗai; amma a garin Lugu, aiki ne kamar kowane aiki, wanda kowa yake iya yi, namiji ko mace. Arewa, shi kaɗai ne ma yankin inda babu wani zancen bauta ko iri a cikin yankunan ƙasar Nijar.
A shekara ta 2004, Tarbiyya Tatali ta samu labarin cewa a Yamai, babbar ma’aikatar yaƙi-da-jahilci da ‘’CARITAS’’ sun tafiyar da wani tsarin horar da mata ga aikin mashin ta saƙa kamar yadda ake yi a ƙasar Burkina Faso ; wani yaro na garin Lugu ya je Yamai don samun wannan horon, kuma ya kawo mashin ta saƙar zamani a garin, har ma aka yi mata wani gida na masamman. Yaron ne yake horar da mata da duk wanda yake so, kuma matan sun yi murna sosai, suna jarraba aikin da guda guda. Amma akwai matsalar cirewar zaruruwa ; watakila wurin hauda mashinɗin ne. don tsoron kar a riƙe mashinɗin a Dogon Dutsi ne kwamitin kula da saƙa yake fatan a gyara ta a nan garin Lugu. To, ko sai yaushe gyaran za ya samuwa ? kafin a magance wannan matsalar, sai a koma irin saƙar da aka saba yi, tare da horar da mata wajen koyon fusa’o’in saƙar da maza kaɗai ne suka iya har yanzu.

Shugabar kowace ƙungiya ta neman ma ƙungiyarta masaƙin da za ya ƙera mashinɗin saƙa ta gargajiya, ya riƙa yin saƙar kuma ya riƙa horar da matan ƙungiyar. Ta haka ne duka ƙungiyoyin yin zaren suka koma yin zaren da saƙar kaɗa. Amma masaƙiɗaya kaɗai ne na garin ; duka sauran na wasu wurare ne daban.
Neman kayan ƙera mashinonin saƙar ne ya kawo matsala. Ba su samuwa nandanan tunda an daɗe da masaƙan gargajiya suka saki aikin saƙa. Sai da aka yi makwanni, kasuwa zuwa kasuwa muna neman tsofin masaƙa don ƙera mashinonin saƙar.
Bayan an daɗe ana bada bayanai da wayen kai, sai aka samu ƙera mashinoni 3 ranar Lahadi 22 ya watan janairu na 2006, kuma aka samu wasu cikin makwanni na gaba. Amma a wuriɗaya aka kafa ukkun, kafin a rarraba su ga shugabannin ƙungiyoyi don sulhunta koyon. Tarbiyya Tatali ta ba kowace ƙungiya kuɗi jika 5 don sayen kaya, ta yi ma mashin ɗinta ado. Adon da launonin da ake sanya ma mashinonin mata, shi ne yake bambanta su da na maza.
Buhun kaɗa yana tashi jika 5 ; kuɗin kaɗin zare, jika 5 shi ma. Ga kowane bandir, jika 5 ake biyan masaƙi, kuma yana ɗaukar kwana 5 zuwa 7 na saƙar. Jika 16 ne ake saida bandir 1 na yadi. Idan matan ne suke yin kaɗin zaren da saƙar, za su yi katihun jika 10 kenan, kuma babu ruwansu da masaƙi.

Wani maɗunki (‘’Tela’’)

An ba wani maɗunkin da ke zaune a Dogon Dutsi, bashin da ya ba shi damar sayen mashin ta ɗunki don yin tufafi da kaɗar Lugu, waɗanda yake sayarwa cikin Arewa da ƙetare.

Horon aikin saƙa

A shekara ta 2007, wata ƴar ƙasar Burkina Faso, ta horar da wasu matan garin Lugu, da na Gugi ; da na Dogon Dutsi, ga yin amfani da abin saƙa na ƙarfe ; ya fi na gargajiya dacewa.

Wajen saƙar, matan suna yin amfani da zaren mashin da kuma zaren da aka yi a garin Lugu.

Tissage