An buɗe wannan ɗakin a Dogon Dutsi, a farkon shekara ta 2008.

Tarbiyya Tatali ta buɗe wanga wuri, na farko a cikin garin don taimaka wa matasa wajen neman sani, da shaƙatawa, da canjin ra’ayoyi.

Matakan buɗe ɗakin na’urar

Ƙungiyar RAEDD ce ta nemo ɗakin a tsakar garin Dogon Dutsi; sai AECIN ta taimaka da bashin kuɗin sayen jacen na’urori na ƙwarai da aka kawo a shekara ta 2009.

An biya bashin wagga ƙungiyar ta AECIN ta hanyar wani taimako da ma’aikatan kampanin Gogol na birnin New York suka bayar, kuma har ma aka ida sauran ayyukan kafa na’urar kamar sayen kujeru da teburori, da wayoyin sadarwa, da sauran su.

A farkon watan Disamba na 2009, an samu wani matashi mai bayar da horo don koyon amfani da na’urorin, kuma za a fara buɗe kumbon yanar gizon ba da daɗewa ba.

Samun horo ga aikin na’ura mai ‘kwaƙwalwa yana jayo hankalin mutane da yawa. A shekara ta 2010, mutane 43 suka rubuta kansu ga wannan horon.

Cybercafé