Unguwa ce a Kewayen Yamai inda yaran talakkawa da yawa masu fama da talauci ba su samu shiga makarantar boko ba. A nan ne wani ‘’huroje’’ da ya fara aiki a shekarar 2002 yake tara waɗanga yara ta hanyar wata ƙungiyar matan unguwar, sai ya ba su horon shekara guda don su samu shiga cikin sauran makarantun gwamnati a shekara mai zuwa.
Makarantar « fata » ta tsaida ayyukanta tsakanin 2013 da 2016.
An sake kafa sabon aji a watan Oktoba 2017. Akwai ƴan makaranta 31, ƴan mata 19 da ƴan maza 12, an samu damar yin wannan aiki da kudaden da AECIN ke biya. Makarantar yanzu dai a sa mata sunan Mahamadu Saidu, wanda ya kafa ta. Mai gudanar da ayyukan ta nuna da cewa inda ana son a yaki rishin zuwa makaranta na yara, to sai an kafa tsarin cin abinci a makarantar da rana. Saboda haka AECIN ta tara kuɗi yin starin.
A shekara ta 2018-2019, an koma makaranta ran 1 ga watan oktoba, ɗalibai 30 ke akwai, ’yan mata 8 da ‘yan maza 22. ’yan mata ba su da yawa saboda ƙanana ne, shekarunsu ba su isa su shiga makarantar unguwa ba. An yi wani annoba ta ƙarimbau a watan Janairu 2019, ta kama mai gudanar da ayyukan makarantar, amma yanzu kome na zuwa daidai. An kafa tsarin cin abinci a makarantar da rana a tsakiyar watan Afrilu. Wannan shi ne lokaci mafi wuyan yanayi na shekara soboda zahi, kuma farashin abinci na karuwa. An kuma kawo ruwa a kusa da aji wanda zai ba da izinin noma lambun makaranta.
