Maganin tamowa ‘’Spirilin’’

Wani tsiro ne da ke fitowa bakin tabkuna a ƙasashe masu yanayi mai zafi. Ana iya shuka shi cikin guraben ruwa kuma ya fito sosai. Sai tsiron ‘’spirilin’’ ya bushe ne ake yin amfani da shi. Ya ƙumshi sinadari iri-iri na gina jiki, da kariyar jiki. Garam 1 zuwa 2 na wannan tsiron a kowace rana, ya isa warkar da yaron da ke da tamowa a cikin sati 5 zuwa 6.

Hulɗa tsakanin ƙungiyar ‘’Antenna Technologics’’ da Tarbiyya Tatali

Antenna Technologic, ƙungiya ce mai gurin yaƙi da tamowa. Ta ɗauki niyyar bunƙasa shibkar tsiron ‘’spirilin’’ a cikin ƙasashe masu tasowa. Tarbiyya Tatali ta amince ta ƙulla hulɗa da wanga tsarin. Tarbiyya Tatali ta ɗauki niyar ba da spiruline abinda ya kai kashi 20 cikin ɗari daga kalarta don taimako zuwa ga masu tamowa.

Gina guraben ruwa da noman tsiron

An zaɓo wurin yin guraben ruwan, an sanya wutar lantarki da pampo, an yi guraben, da magewaya, da ɗakuna, kuma an shibka tsiron cikin guraben.Akwai mutumen da ke motsa guraben a kowace awa, kuma kowace rana. An shibka ‘’spirilin’’ a farkon lokacin zafi na shekara ta 2007, kuma aka fara ɗibar shi. Malaman da ke yi wa yara masu tamowa magani a Dogon Dutsi, sun yarda da ingancin tsiron ‘’spirilin’’; yana gaggauta warkewar yaran da aka riƙe a lilita ; a Nijar yara masu ɗimbin yawa ne suke da tamowa.

Balas na tattalin arziki mai wuyar samu

Yanayin dubu biyu da goma

Akan samu hiya da kilo talatin ko wane wata. Amma tsada gare shi, kuma mutane ba su saba yin amfani da shi ba. A fuskar abinci, masamman na waje mata da yara, hakin ‘’Spiruline’’ yana da mahimmancin gaske. An samu taimako don a shigar da ‘’spirilin’’ ɗin da aka noma wajensauran gidajen likita da ɗakunan magani, kamar na kwamin ta ɗankatsani.

Daidaiton arziki mai wuya

Lambun spiruline ya samu kimanin kilo 42 wata duk cikin watanin 15 na baya. Cikin wannan a ke talahwa ma likitan Dogonduci da kilo 8 don kokowa da tamowa. Cinikin yakan tashi kimani kudin kilo28. a cikin su RAEDD tana saida kilo 16 a Niger kuma kilo 12 akan ceto ga mara galihu. (Sune su kan hito daga Croix rouge, Antenqa technologie da kudaddin da AECIN ke karɓa). Spiruline da ke aje ta kai kimanin kilo 175 saidai kuma lambun bai iya biya albashin ma’aikata ba. Akan yi gorgodon albashin wata shida ne ma’aikatan ke bin lambu. Akan haka ne Antena Technologie da kungiyar AECIN za su ‘daukar mahimmin mataki don ‘bunkasa saide saidan spuriline a Yamai.. sai kuma wata hanyar da ake tsamanin taimakonta ita ce kungiyar lafiyar uwa da ‘da da matar shigaban ƙasa ke wakilta.

Inda aka kwana watan augusta 2012

Bayan ɗaukar ma’aikaci mai kula da saida spiruline da kuma saida spiruline akan farashi mai rahusa da taimakon talahi daga Faransa, akan samu ajewar kilo 250 bayan albashin ma’aikatan lambun yana taruwa kambacin a biya su.

Bayan an samu kwararan likita ko dokta a kowane lardin ƙasar Dogonduci, saidawa da rahusa yakan ɓunkasa. Akan taimaka ma yara masu fama da tamowa kambacin yuro 0,8 ga ko wane yaro sai dai kuma kuɗin su shige kamar yuro 2 (CFA 1250).

Akan saida spiruline cikin parmasin Nijer da wani cinikin kai da kai a Faransa wanda har ya ba da dama a hihitar da kasuwancin da tanadidi. Yawan abinda aka aje ya kai kimanin kg 170 saidai kuma kash ma’aikata ba su samun albashinsu.

An ƙarfafa halin albashi a hankali a shekarar 2014, tare da samun ajiyar kilo 55 : Ana saidawa kashi kashi. An fi ɓunkasa saidawa da taimako. An ba da kilo 80 a gidan likita ta maras lafiyar AIDS ( game da taimakon kuɗin AECIN )

Halin da ake ciki a shekarun 2014-2016

A yanzu dai babu bashi albashin. An samu hanya ta saida maganin tamowa akan farashi mai rahusa cikin ɗakunan shan magani na garuruwan. Wannan dai game da taimakon kuɗin AECIN.

Yanayin a shekarar 2017-2018

Ƙaddamar da Antenna Technologie Nijar ta kara inganta kasuwancin wannan maganin tamowar a Niamey. Hanyoyin farashin-tallafin kuɗi ya takaita. An sake fara yin Kyautar agaji a asibitin Dogon Dutsi. A karshe, an yi aikin gyare gyaran gonar da kayan aikin lantarki na makamashin rana tare da kudade daga Kamfanin ruwa na Nijar. Bidiyo.

Yanayi a cikin 2020

Kodayake yanzu ba ta ba da gudummawa don tallafawa gonar spirulina, AECIN na ci gaba da lura da wannan aikin ta hanyar rahoton gonar na kowane wata. An samu kilogiram 156 a shekarar 2020 (idan aka kwatanta da kg 328 a shekarar 2019). Daga cikin kilogiram 46 aka kaiwa asibitin Dogon Dutsi kuma an ba da kilogiram 45 zuwa wata cibiyar abinci mai gina jiki a Yamai da kuma wata kungiya mai zaman kanta a Zinder. Za’a tabbatar da makomar gonar spirulina tare da wadatar da kantuna na dindindin.

Tsayawar ayyukan a 2021

Ba a sami mafita ta dindindin na tattalin arziki ba, gonar ta dakatar da ayyukanta a cikin 2021.

Construction d’un bassin à la ferme de spiruline
{{}}