An kammala wannan mataki.

Kwamin 10 ke cikin dapartaman Dogon Dutsi, kuma kowace tana da kwaleji guda. Kuma ya kasance yawancin ƴan makarantar, daga garuruwa masu nisa da kwaminonin suke zowa ; wasu suna yin tafiyar kilometir 10. Saboda haka Tarbiyya Tatali ta taimaka wa yaran da kekunan hawa.

Tattarar kekunan hawan da aika su

Waɗannan ƴan goyon bayan AECIN suka ɗauki nauyin bada labarin kuma da tattara jacen kekunan a Faransa. Kuɗin shaidar shiga tsarin (yuro 1 a kowace takardar shaida) sun bada damar biyan suhurin kekunan. An yi wala walar a ranar 9 ga watan mayu 2007 inda wani ɗan makarantar ‘’Lise’’ na Rennes ya ci sabon keken hawa.

Fiye da keken hawa 700 aka tattara. A cikin su an aika 350 ta hanyar jirgin ruwa a ranar 9 ga watan mayu 2007, tare da hasashen zuwansu a Dogon Dutsi a farkon watan juni. Bayan haka akwai tayoyi manya da ƙanana 160, kayan sance taya 3 har kashi 10, pampo 10 na takawa da ƙafa, ‘’shambir’’ 210 sabbi gal, ƙumussa 20 na kiluluwa daban daban. Za a yin amfani da waɗannan kayan don a fara koyon gyare-gyare.

Wuraren gyara da ba da horo

A Nijar, ƙwararrun ƴan gyaran keken hawa sun horar da kimanin matasa 20 da suka zo daga dukan kwaminonin. A ƙarshen horon, an damƙa ma kowanne kayan aikin domin ya rungumi sana’ar gyaran kekunan hawa. An gudanar da wannan horon a cibiyar bada Makarantar horo ga ayyukan ci-gaban al’umma (CFDC).

Ɗorewar wannan aikin

Kowace kwamin za ta samun kekunan hawa da za a damƙawa a hannun kwamitin tattali, kuma majalisar babban taron uwayen ƴan makaranta ce za ta ƙayyade yadda za a yi da kekunan (a sanya su haya, ko a sayar, ko a bada haya har mutumen ya biya kuɗin keken). Kuɗin da aka tara ne za su yi amfani wajen gyaren-gyaren kekunan ko sayen wasu.

Aiken kekuna na biyu

Wasu kekunan sun zo a ranar 16 ga watan faburairu 2008. Aike na biyu ne da hurojen ya yi ; jimillar kekuna 600 kenan da hurojen ya aika. A wannan aiken, mun samu kyaututtuka da dama, a misali daga kwamin ta ‘’ Cesson-Sévigne”.

Cibiyoyin ba da horo kan ayyukan ci-gaban al’umma

Zuwan kekunan 500 daga Faransa ya bada damar kafa cibiyoyin bada horo kan ayyukan fannin gyare-gyare, da na noma, da sauran su, a cikin kwaminonin 9 na dapartaman Dogon Dutsi.

Montage de vélos