An kammala wannan mataki.

Ƙ ungiyar haɗin kan mata da ake ce ma ‘’Niyya da ƙokari’’ take gudanar da wannan aikin.

Mata suna raya hilaye

Tarbiyya Tatali ta yi ziyara ta farko a garin ‘’Wasa-da-hatsi’’ a shekara ta 2003. Hakan ya ba ta damar saduwa da ƙungiyar haɗin kan matan ‘’Niyya da ƙokari’’ albarkacin wani gagarumin taron mata da yawa suka halarta. A nan ne muka ji irin jan ƙoƙarin da matan garin ‘’wasada-hatsi’’ suka yi wajen raya hilaye bisa tudunnai ba tare da taimakon ƙetare ba. An shuka itacen ƙwaro, da magarya, da noman gujiya.

Dangance da kafa tsarin ƙananan busussuka

Wannan taron ya ba mu damar ƙara wa tsarin himma, kuma da ƙarfafa aikin ‘’Niyya-da-ƙokari’’ ta hanyar girka asusun ba mata ƙananan basussuka don bunƙasa ayyukan tattalin arziki daban daban, kamar yin man guyiya, da wasu ƙasuwanci. Bayan haka, ƙungiyar ‘’Aide et Action’’ ta ba matan garin ‘’wasa-da-hatsi’’ wani inji na ɓarar gujiya.

CEDEFhausa