Gwamnatin Nijar ta ɗauki likitoci da dama domin su yi aiki cikin ƙauyuka (farkon 2012).

Cikin jihar Dogonduci, mai jama’a kimalin 680 000 (adadin 2011), kowace kwamin tana da likita cikin gidajen likitocin, alhali a da ko a likitar Dogonduci kadai ake samunsu.

Likitocin suna bukatar kayan aiki don cima gurinsu sosai.

Wannan tsari, an yi shi ne da taimakon jihar Bretagne, kuma da kuɗin Tarbiyya Tatali da kanta, don sayen kayan aiki na ofis kamar (tebur, kujera, na’urar lissafi, maratayin kaya na karfe, abun kasa takardu, da takardu, abun gama takardu, abun huda takardu, agogon bango) da kayan aikin likita ( tebur na yin magani, akwatin bandeji, akwatin kayan haifuwa, na’urar daukar sukari cikin jini, na’urar daukar hawan jini, na’urar daukar naujin mutane, tire).

Kuɗin kayan aikin likita ɗaya euro 1500 (CFA 1 000 000) ne.

An tura farkon likitocin da suka samu kayan aiki a gidajen likitocin Dankatsari, Arewar Dogonduci, Matankari, da Sukukutane. Likitoci na Kieche, Guecheme da Kore Mairuwa sun samu kayan aiki game da gudumuwar Kungiyar Total.

Abin takaici likitoci uku kawai ke akwai a sashen Dogondutchi a farkon 2018: biyu a asibitin Dogondutchi dayan a Dankatsari. Likitocin da aka kai a sauran yankunan karkara ba su tsaya ba.

A karshen shekarar 2019, likita daya ne ke akwai a sashen Dogondutchi, yana aiki a asibitin Dogondutchi.

A shekarar 2020, an dauki ma’aikatan lafiya 1,500 ciki har da manyan likitoci 250 saboda annobar COVID, kuma likitoci shida suna nan a sashen Dogon Dutsi, 3 an tura su asibitin Dogon Dutsi, likita mace a Dankatsari, ɗaya a Dogonkiria da ɗayan a Sucucutane.