Game da shawarwari tare da RAEDD, AECIN ta gabatar da aikin inganta samar da ruwa a ƙauyukan arewacin sashen Dogon Dutsi, ga Sashen Directa na neman ruwa da tsaftar muhalli wato hydraulic da kuma majalisan gari na ƙananan hukumomin biranen da abin ya shafa.

Ya haɗa da :

  • Wani wurin samun ruwa a ƙauyen Goriba (garin Matankari) ana haka ruwan ne da hasken rana da wani karamin rufin ruwa wanda ke kula da ba da ruwa ga pompo biyu,
  • Wata rijiyar zamani a ƙauyen Birbiro (garin Dogonkiria),
  • Horar da masu amfani da wurarren samun ruwa da manajoji masu kulawa da rijiyoyin.

An samun yin wannan tsarin tare da taimakon kudi na kamfanin ruwa na Loire-Brittany, na yankin Bretagne, na Rukunin ruwa na Rennais, na ƙasar Nijar, na AECIN, da kuma na yawan mutanen da abun ya shafa.

An yi bikin samun wurin tsarkakun ruwa na Goriba a ranar 31 ga watan Disamba shekarar 2018. Ana cikin hakar riyiyar Birbiro.

An samu nasarar karɓar wurin samun ruwa na Goriba a ranar 31 ga watan Disamba, 2018 da kuma kafa Ƙungiyar Masu Amfani da Harkokin Watsa Labaran Jama’a a Goriba, ran 12, 13 da 14 ga watan Fabrairu 2019.

A 2020, an gyara rijiyoyi biyu a ƙauyukan Wutchia (Karamar Hukumar Dogonkiria) da Kufa (Karamar Hukumar Matankari).

Puit de Birbiro