A nan ana nufin samar ma kowane yaro na ƙanannan makarantu dukan littattafan da ya kamata. Wannan ƙoƙarin, an fara shi a shekara ta 1997 a cikin makarantu 8, yawancin su cikin yankin Dogon dutsi, kuma yanzu an ci gaba da haka a cikin fiye da makarantu 56, inta aka raba dubunnnan littattafai da aka sayo. A nan Nijar ne aka wallafa su dangane da tsare-tsaren koyarwa da gwamnati ta ƙayyade. A cikin iyalai da yawa, karon farko ne yaro ya zo da littafi cikin gida.
Matakan tafiyar da aiki
Mutanen da ke cikin kwamitocin tattali, su suke jayo hankalin dukan uwayen da ɗiyansu suka isa shiga makaranta domin su zuba kuɗin hayar littattafai. Har tsawon shekarar, littafin zai kasance a hannun yaron, zai riƙa aiki da shi a gida a gaban idon uwayen , ko da ba su san kome ba.
Kwamitin yake tashi-ka-faɗin tattara kuɗin hayar littattafan, ya duba halin taimakar uwayen da ba su da su, da hanyoyin yin amfani da kuɗin. Ta hanyar masayar littattafan ne kwamitocin suke samun waɗanda suke buƙata.
Sakamakan da aka cim ma
Mizanin rubuta yara makaranta, da na cin nasarar shiga ‘’kwaleji’’ sun ƙaru sosai. Kuɗin hayar littattafai suna bada damar sayo wasu. Bayan haka, makarantun farko suna samun isassun kuɗi na kansu tun shekara ta 2004.
Hakan yana ba mutanen garin da malaman makaranta damar hangen wasu ayyuka kamar bunƙasa ayyukan hannu, da ƙara faɗaɗa lambun makaranta, da sake maido irin shibkar wasu tsire- tsiren da ba a gani yanzu, da sauran su.
Yaɗuwar tsarin ga wasu ƙananan makarantu
Da farko, tarbiyya Tatali ta fara saka kuɗi tare da samun taimakon daga birnin Rennes. San nan ƙungiyar ‘’Aide et action’’, bayan wani nazari mai zurfi, da ganin sakamako mai kyau da hurojen ya samu, ta ɗauki niyyar bayar da kasahin kuɗin yaɗa wannan tsarin daga shekara ta 2003 zuwa 2004, a cikin makarantu 8. Bayan wannan, ƙungiyar hulɗa da ƙasar Kanada ta ƙara yaɗa tsarin a cikin wasu makarantu 36. Bugu da ƙari, Tarbiyya Tatali ta tallafa ma wasu ƙungiyoyin da suka buƙaci bin wanga hanyar. Su ne : ƙungiyar taimakon juna ‘’solidarité Niger’’ da ta ‘’Mouvement solidarité des Lycéens du collège Mariama’’ Kenan haɗin kan ƴan makarantar ‘’Lise’’ Maryama na Nijar, da ƙungiyar ‘’côtés d’Amor’’ ta Agadas da jahar ‘’côtés d’Amar’’.
Yaɗuwar tsarin ga wasu makarantun ‘’Kwaleji’’.
Akwai babbar matsala ta rishin littattafai a cikin makarantun ‘’waleji’’ da ‘’lise’’; matsalar za ta ƙara tsananta cikin ƴan shekaru masu zuwa saboda bunƙasar ƙananan makarantu. A shekara ta 2005, ƙungiyar Tarbiyya Tatali tare da taimakon ‘’dapartama na” côtes d’Armor’’ ta gudanar da wani gwaji a cikin jahar Agadas. Kuma ta yi ɗakin littattafai don amfanin ƴan makaranta da malamansu a cikin ‘’kwaleji’’ biyu na Dogon Dutsi. Hakan ya yaɗu a cikin ’’kwaleji’’ biyar a sakamakon hulɗa tsakanin birnin Zandar da na ‘’le val de Marne’’.
Littattafai a cikin makarantun ‘’Lise’’
ƙungiyar ‘’RAEDD’’ tana wallafa wani littafin koyar da faransanci wanda ya ƙunshi matanan da faransawa suka rubuta, da kuma waɗanda ƴan Nijar suka rubuta. Makarantar ‘’Lise’’ ta Dogon Dutsi za ta amfana da littattafan tare da tallafin birnin ‘’Rennes’’.
