Wannan gatanar ta fito daga littafinmu na gatannai mai sunan ‘’il était une fois au Niger’’ a turance, wato « Nijar, a wani lokaci’’. Kuna iya samun littafin a cikin kantinmu.

Taƙadarin yaro

An yi wata mace wadda ta riƙa kuka da rashin samun haifuwa, kuma tana roƙon Allah ya ba ta damar samun ɗa ko ɗiya. Sai kuma Allah maji roƙo ya ba ta haifuwar ɗa namiji mai kyau, wanda ake kira da sunan Daɗi, kenan wanda aka daɗe ana jira.

A kwana a tashi, yaro ya girma har ya zama mai taimakon iyayensa. Wata rana, Maigarin, maƙetaci ne, ya umurci baban Daɗi da tatsar mazan shanu. Baban Daɗi ya je da shanun wurin ɗansa inda ya faɗa masa wannan umurnin da Maigari ya ba shi. Da jin haka, ran Daɗi ya ɓaci ; sai ya ɗauki gatari ya tafi gidan Maigari. Daga zuwansa, sai ya shiga sare iccen da ke a ƙofar gidan Maigari ; rassan da kunnuwan iccen suna faɗowa. ƙaran faɗauwarsu ya sa Maigarin ya zaburo, ya ce :

  • Kai Daɗi ! Mine ne kake yi wa iccena?
  • Babana ne ya haifu, kuma zan kai masa iccen yin ruwan zafi. Inji Daɗi.
  • Ƙaƙa namiji yake iya haifuwar ɗa? Inji Maigari.
    Shi kuma Daɗi ya ce :
  • Yaya ake iya tatsar mazan shanu ?

Wagga amsa ta ɓata wa Maigari rai sosai, sai ya yi niyyar kashe Daɗi.
Sai ya umurci fadawansa, su yi rame mai zurfi su bunne Daɗi. Daga jin haka, sai shi ma Daɗi ya yi wani rame mai haɗuwa da ramen Maigari. Da ranar bunne Daɗi ta zo, sai fadawa suka sanya shi rame, suka maida ƙasa, suka rufe. Tun daga nan, kowa ya tabbatar da Daɗi ɗan lelen uwarsa, ya mutu Amma cikin ɗan lokaci, sai fadawa suka tsinkayi Daɗi ya taho wajen su. Abin da namaki, Daɗi bai mutu ba.
Ran Maigarin ya ɓace matuƙa, kuma ya sare wa al’amarin wannan yaron. Amma sai ya ɗauki niyyar bin wasu hanyoyi daban don kashe Daɗi. Sai ya kirawo fadawansa na kusa, ya umurce su da su sanya Daɗi a cikin wani buhu, su jefa shi cikin wani tabki.

A wannan gamin ma, sai wani kado ya kawo buhun bakin ruwa a sunce, ya tsirar da Daɗi. Kuma sai ga Daɗi a fadar Maigari. Da Maigari ya gane da ya yi karo da taƙadarin yaro, sai ya ɗauki niyyar barin yi wa Daɗi mugunta. Daga nan Daɗi da Maigari suka zama manyan aminai.

Abin aƙida shi ne : ‘ƙamar yadda ake faɗi a gargajiyarmu, idan ka tsira ga muguntar wani, amininsa kake zama.

Makarantar boko ta Made.

Il était une fois au Niger