An fiddo wannan gatanar daga littafinmu na gatanai wanda ya ƙare mai sunan “A l’école des contes nigériens” wato “gatanan Nijar a makarantu”, kuna iya samun littafin na biyu mai suna ‘’Il était une fois au Niger’’ a cikin kantinmu.

Halin kishi

An yi wani mutun mai mata biyu. Ƙaramar matar tana da ƴar ɗiya, amma sai ta mutu ta bar ɗiyar a gidan, har ta girma. Ita take yin dukan aikace-aikacen da aka sanya ta.
Wata rana sai ta ji sunan wani ɗan sarki mai sunan Abuduka. Lokacin da kishiyar uwarta ta yi niyyar tafiya kasuwa, sai ta ba ta dala 5, ta ce Kishiyar uwar ta sayo mata Abuduka. Kishiyar uwar ta yi ta bincike a kasuwa, tana cewa :

  • Ku saida mini Abuduka.

Ko’ina a ce :

  • Babu Abuduka a nan ; tafi gaba, za ki same shi.

Da ta iso inda Abuduka yake, sai ta ce :

  • Ku saida mini Abuduka.

Sai wani mutum ya tashi tsaye, ya ce :

  • Ni ne Abuduka ; ki tafi gida, zan iske ki.
  • A’a , inji matar ; diyata ce ta ba ni dala 5 don in sayo mata Abuduka, in kai mata.
  • Eh ! na sani, ina iske ki a gida.

Ko da ta dawo gida sai ta ce wa ɗiyar :

  • Kin san Abuduka mutum ne ko ?

Sai ɗiya ta sadda kai, ta yi wata ƴar magana can ƙasa.

Da dare ya yi sai Abuduka ya zo gidan, ya sallama.

  • Salama Allekum.

Sai ya koma share guda, suna hira da yarinyar. Da suka ƙare hirar, sai ya tafi gida.
Wansafake sai ya dawo da zinare ya sanya a ɗakin yarinyar. Sai ɗakin ya yi kyau, yana walƙiya kamar tauraru a samaniya. Sai kishiyar uwar ta ce :

  • Sai na ga ɗakinki.

Ko da ta duba cikin ɗakin, sai kishi ya kama ta, sai ta tafi kasuwa ta sayo allurai ta sanya su bisa gadon da Abuduka yake kwantawa idan ya zo wurin hira.
Da Abuduka ya zo ya kwanta, sai alluran suka sossoke shi. Da suka ƙare hira, sai ya koma gida ; amma ko da ya isa gida, rashin lafiya mai tsanani ta kama shi.
Wata rana sai yarinyar ta ce :

  • Kai, Abuduka ya daɗe bai zo gidanmu ba ; bari in tafi garinsu in gani !

Yarinyar ta yi tafiya mai nisa, kuma ta koma Badosa. A gaban wani icce, sai ya ce mata :

  • Abuduka ɗan sarki yana fama da wata cuta mai tsanami. Bari in ba ki magani. Ki ɗebi ɓawana da za ki jiƙawa a cikin wata yar ƙwarya, sai ki ba shi ya sha. Idan ya sha, zai warke. Yarinyar ta iso garin, ta zo fadar sarki, ta yi tambaya.
  • Abuduka ba ya da lafiya Inji Sarki.
  • Ku bar ni in wuce, in ba shi wani magani.
  • Duka sayun da ya sha ba su yi magani ba, sai ke wanga Badosar za ki cewa kina da magani ! to je ki gane shi, ga shi can kwance.

Sai ta shiga ɗakin, kuma ta nema a kawo mata ƴar ƙwarya da ruwa a ciki. Ta jiƙa ɓawan ya sha.
Ko da Abuduka ya sha, sai ya samu lafiya. Ya ba yarinyar zobensa na zinare. Yarinyar ta koma gida kuma ta maido siffarta ta farko.
Amma daga baya, sai sarki ya aika fadawansa su kashe yarinyar.
Da suka je, sai suka ga zoben zinare na ɗan sarkin a ɗakinta. Abin ya ba su mamaki, sai suka koma wurin sarki suka ba shi wannan labarin.
Sarki ya umurce su da su koma su kawo yarinyar. Da suka kawo ta fada, sai sarki ya tambaye ta ; ita kuma sai ta ba shi bayanin duk abin da ya faru : kishiyar uwarta ce ta yi dalilin da Abuduka ya shiga wannan mawuyacin halin.
Sai sarki ya gane komi, kuma ɗan sarki ya aure yarinyar.

Gatana ce ta Nijar wadda makarantar Ahole ta gabatar a gasar da ‘’Aide et Action’’ da RAEDD suka shirya ga bikin nunin al’aun gargajiya na gatan gatan.
Mai gatana : zabairu Dan zama
Ƴan makaranta : Bumaminu Abbu, Ibrahim Koshe, Mahamadu Abdurahaman, Aziz Barke, Hasira Halidu, Manyama Abdu.
Malamai masu kula da tsarin : M. Bubakar Sani, Malama Aishatu Abba.

A l’école des contes nigériens