An kammala wannan mataki.
Sakamakon bincike
Ƙungiyar ‘’RAEDD’’ ta yi lura da ƴan makaranta da yawa ba su iya karatu da rubutu ba a ƙarshen aji na 6 na ƙananan makarantu. Hakan ya zama babban cikas ga makomar yaran.
Aikin da ‘’RAEDD’’ ta tsara
Bayan gwajin koyarwa cikin babban hutu a shetarar 2007, a shekarar 2008 sai dukan kwaminonin 10 na ‘’dapartaman’’ Dogon Dutsi suka amince da a zo a riƙa yi musu wanga aikin.
Ana aiwatar da wannan tsarin ba tare da tallafin kuɗi daga ƙetare ba. Guirinsa shi ne, a cikin wata 1, a ƙarfafa horo don shawo kan matsalar rishin iya karatu da rubutu.
Hukumomin kwamin suke nuna wa uwaye amfanin rubuta yaransu ga wannan tsarin, kuma su zaɓo wanda za ya tafiyar da koyarwar. Shi kuma shugaban ƙananan makarantun, ya bada d’akin karatun, da kuma kayan aiki kamar alli, da sauran su.
Uwaye ba su biyan kuɗin rubuta yaransu, sai dai suna sayen littafin karatu da rubutu mai darussa 30, a wajen ‘’RAEDD’’. Jikka 2 ne kuɗin littafin ; a ciki sai a ware ma malamin dala 100, kuma ɗari 3 na ruɓinya littafin.
ƙungiyar tana keɓe ranar horar da malaman a game da yadda za su yi amfani da littafin, kuma ta biya su dangance da yawan littattafai da suka sayar.
Wasu kwaminoni sun shaida rubuta ƴan makaranta 50.
Watan ‘’Agusta’’, wata ne mai matsalolin ƙarancin abinci kafin a fidda albarkatun noma. Kenan sai an nemi hanyar taimakar uwayen da ke son rubuta ɗiyansu.
A shekarar 2009, ba a tafiyar da wannan tsarin ba, a dalilin hatsarin motar da ya shafi malamin ‘’RAEDD’’ mai kula da tsarin.