RAEDD (Ƙungiya mai kula da ayyukan horarwa don ci-gaba mai ɗorewa) kungiya ce ta Nijar da aka kirkira a shekarar 1998.
Tsari.
RAEDD ya hada da:
- Babban sakatare da ma’aikata biyu.
- Akwai wani reshe kuma a Dogon Dutsi mai ma’aikata huɗu.
Kawance.
Tun daga 1998 suna da yawa da bambanci. Misali:
- Hukumomin cikin gida a Faransa: gundumomin Rennes da Cesson-Sévigné, Yankin Bretagne, Kungiyoyin majalissar Côtes d’Armor, Ille-et-Vilaine, Val-de-Marne, Rennes Métropole ....
- Kasar Nijar a fannin samar da sinadarai, tsabtace ruwa da kuma samar da makamashi,
- Ma’aikatar ruwa ta Loire Bretagne, Kungiyar Departement ta makamashi 35, Ma’aikatar ruwa ta Rennais,
- Ma’aikatar Harkokin Wajen Faransa, Ofishin Jakadancin Kanada, Ofishin Jakadancin Spain
- Kungiyoyin masu zaman kansu kamar Gidauniyar Stromme
- kungiyoyi na duniya kamar Asusun Majalisar Dinkin Duniya na Jama’a
Adareshi :
RAEDD Tarbiyya Tatali
c/o Seiyaba Elhadj Saidou
BP : 2554 Niamey, Niger
Mel : raedd@tarbiyya-tatali.org