Tushensa

A golgodo dai, fim na Nijar ya fara a shekarar 1941 lokacin zuwar injiniyan gina kodarko Malam Jean Rouch a Nijar. 1947 ya shirya fim mai suna “au pays des mages noirs” ma’ana « garindodanin diba ” da kuma « gorgodonkoyin rawa masu safara na Wanzarbe» a 1949.
Abubuwan sun samu faruwa lokacin da shi Jean Rouch ya sadu da wani tsohon soje da suka yi yakin andochin tare malam Umaru Ganda shahararen ɗan wasa fim kamar cikin fim ɗin “Moi un noir” (1957) da Jean Rouch ya tsara. A kambacin fassa’a sa Malam umaru Ganda ya kore sosai a fannin fim; Bayan zama shahararen ɗan wasa ya zama mataimakin Ruch kafin ya zama ɗan Nijar na farko mai safarada fim. Allah ya yi ma Malam Jean Ruch tikawa a Nijar lokacin hatsarin mota cikin daren 18 zuwa 19 febrari 2004.

Korewa da Zarcewa

An fara sani suna Nijar a fannin fim lokacin da shahararen ɗan fim ɗin nan Mustapha Allassane ya samu lambar yabo masu zane zane a kompla farko ta wasan al’adun galgajiya da aka yi a baban Birnin Dakar a shekarar 1966. Sai kuma fim ɗin Umaru Ganda mai suna Cabacabo, fim ɗin da aka yaba a kompla fim na Canne (Faransa 1969) sai kuma samun lambar yabo a Moscu (Rasha 1969).
A wasar FESPACO ta 3 na Burkina Faso ran 12 ga watan maris Umaru Ganda ya samu kiwan Yabo na lambar Etalon de Yenenga wanda kowa ke hangin samu. Yabon ya samu ne daga fim ɗin mai suna “Wazou polygame”. Saboda sunan Nijar da ya daga sama an sa ma shahararen gidan wasa nan na Yamai “Gidan wasan al’adun galgajiya Umaru Ganda”
Haka zalika yabo ya samu kambacin wani fim mai tassiri na Gatta Abdourahamane (1979) saboda fim ɗin shi “Gossi” dai aka sanar da yadda ake yi ma samari da ‘yan mata yanka ko kungulu. Yan Nijar dayawa ne suka samu yabo kamar su Zalika Souley a Tunis, Djingareye Maiga, Mamane Bakabe, Inusa Useini, Mustapa Diop da kingin su. Sai dai kasch, lokacin da sanin kasa Nijar ya fara bunkasa sosai sai ya zamanto ‘yan fim ba su samun talahi daga Gwamnati ba.

Aniyar farfadowa

A wata na 8 shekarar 2005, gungun Tarbiya na Yamai sun yi fim ɗin su na farko mai suna “Tuwo ya yi Magana”. Ma’ana wannan fim yakan kwatantawa yadda wasu al’adu ke hana ruwa gudu a fannin hakin ɗan adam, bunkasa tatalin arzikin ƙasa da kingin su. Tuwo ya yi Magana littafi ne wanda Mme Abdu Uma ta walafa a halshen hausa.
Tun lokacin nan dai sai aka ganar da bunkasar matasa dayawa da ke da kuzari da fasa’a da yin yunkuri kamar Malam Sagiru (Mai hwarautar iska, kudin abinci, ɗan Afirka a Annecy, akuya mai barna, rigar zamani da kinginsu) Sani Elhadji Magori, Siradji Bakabe, Adamu Sadu, Isufu Magagi da sauransu kamar Aicha Macky.
An samu yin wannan ne tare da aikin wajen sarafa fim na Jean Rouch.

An tsamo shi daga wikipedia.

Damure Zika shahararen ɗan wasa na Jean Rouch

 

Dans cette rubrique