
Haɗin kai yana faruwa tsakanin al’ummomi masu ra’ayi ɗaya, ko guri ɗaya, kuma yana tare da taimakon juna.
Kamar yadda ƙungiyar raya ƙasashe masu tasowa ta majalisar ɗinkin duniya ta bayyana, Nijar tana ɗaya daga cikin ƙasashen da suke a bayan fage a fannin jin daɗin rayuwa.
Duk da Nijar tana da wadatar mutane da al’adun gargajiya, al’ummar tana fuskantar talauci, da rashin ruwa, da na abinci, da na tabbatar da horo da magungunna.
Wasu mutanen ƙasar waɗanda suka samu horo, ƙwararru kuma masu niyya, suna kokowa har kullum don kyautata rayuwar al’ummomin karkara da na birni. Waɗanga mutanen da ke taimaka wa al’ummomi wajen ci-gabansu, suna tare da al’ummomin, tunda harsunansu da tabi’unsu da ka’ idojin zamankakewarsu, da kuma aƙidansu, ɗaya ne. Sun fi kowa sanin abubuwan da ya kamata a gudanar na ci-gaba tare da al’ummomin domin jin daɗinsu.
Abinda ba su da galihu sune hanyoyin samun kuɗi, da tallafin ɗabi’a

