Gudunmuwar kuɗi ko yaya take tana da amfani.

Bada jacen abubuwa, ba kullum yake dacewa ba.

Aiko mana azazzun magungunnan, da jacen tufafi da na littattafai, bai dace ba kan dalilai da yawa.
In don mun kwashike kayan da muka gaji da su ne daga cikin akwatinanmu, mu aika a ƙasashe masu fama da rashi, to haka ba wani abun kirki ne muka yi ba, kuma ba a iya kiran shi cuɗayya.
Kuma suhurin kayan yana da tsada saboda nisa tsakanin Nijar da ruwan teku; kenan babu tashar jirgin ruwa. Mun ƙwammace mu sayar da kayan jacen wurin wantare, tun a can Rennes, san nan mu aika kuɗin a Nijar inda za su yi amfani wajen sayen abubuwan gida da suka fi dacewa, kuma ta haka sai a ƙara bunƙasa kasuwanci.

Wasu abubuwan suna da amfani

Daga cikin kayayyakin, wasu suna da amfani a can, kamar luletin gani, waɗanda ba a ƙerawa a can. Kenan ya cancanta a nuna ƙarfinsu.

Magungunna

Yana yiyuwa magungunnan da ba a yi amfani da su ba, ba su dacewa sosai da yadda ake buƙatar su a Nijar, kuma suna iya zowa a hannun mutanen da ba su da cikakken horo ; har a jayo wani ciwo maimakon yin magani. Magungunna kamar su ‘’aspirin’’, su ne suka fi buƙata ; amma su ma sai da kuɗi.

Tufafi

Tufafin ɗari ne suka fi amfani saboda sanyin da yake sabkowa da marece ko da dare a wani lokaci, su ma dai aika su ke da tsada.

Littattafan ƴan ƙananan makarantu

Littattafan ƙananan makarantun Faransa ba su dace ba da tsarin koyarwa na ƙananan makarantun Nijar. Kenan ya fi dacewa a aika kuɗin domin sayen littattafan da suka dace.

Littattafan ‘’sakandari’’ (‘’se’eje’’ da ‘’Lise’’)

Littattafan ƴan makarantun ‘’sakandari’’ wato ‘’se’eje’’ da ‘’Lise’’, da littattafan adabi, da ƙamusoshi da saran su, ana buƙatarsu sosai saboda ƙarin sani, sai dai babu su sosai. Kenan ana iya aika da yawa a can, ko da yake kuɗin aikawar sun yi yawa.

Photo d’Alain Roux