A Yamai
Hedkwatar RAEDD tana zaman aiki a gundumar Tallague .
A garin Dogon Dutsi
An buɗe ofushin a shekara ta 2003. Ta hanyarshi ne ƙungiyar take tsara ayyukanta, kuma take samun cuɗayya da al’umma kodayaushe.
Ofushin yana kusa da kusuwar garin; nan ne ma’ajiyar kundayen ƙungiyar, da na dukan bayanan da suka shafi garuruwa inda Tarbiyya Tatali take gudanar da ayyukanta.
Idan wakilan garuruwan suka zo kasuwa, sukan biyawa a ofushin don tattaunawa kan ayyukan da ake ciki. Hakan yana sawa a riƙa bin ayyukan sau-da-ƙafa, da garuruwan suna tafiyar da ayynkan ci-gabansu da kansu.
A garin Agadas
Kamar irin na Dogon Dustsi, an buɗe ofushin Tarbiyya Tatali a garin Agadas, amma ta hanyar huld’a tsakanin wani gari da ake ce ma ‘’côtes d’Amor’’ da dapartama na Cirozerin.
A garin Tawa
Tun shekara ta 2007 ne aka bud’e ofushin a garin Tawa.
Wannan ofushin yana taimaka wa ƙananan makarantu 3 na garin Kau cikinɗapartaman Cintabaradan, ta hanyar asusun yaƙar talauci na hukunar ci-gaban ƙasashe ta ƙasar kanada, cewa da ‘’ACDI’’.
Ayyuka 3 ne ake tafiyar da su :
- ,Samar ma kowaneɗan mataranta littafi bisa kowane fannin ilimi
- Kyautata mahalli a cikin matarantu ta hanyar samar da ruwa, da gina makewaya, da killace makarantun, da shuka itatuwa
- Kafa tsarin kiwo da karatu.
A gain Yamai
Akwai wani ofushi a Yamai, har da magatakarda, saboda tafiyar ayyukan cibiyar ƙungiyar.