A Nigar, samun tsakakun ruwan sha, babbar matsala ce ga mata a cikin rayuwarsu ta yau da gobe. Yawancin lokaci, sai mata ko ƴan mata sun yi tafiyar kilometir da yawa don neman tsarkakun ruwan sha. Akwai isassun ruwa ƙarƙashin ƙasa, sai dai zurfi.
Sanin tsabta,hanya ce ta inganta lafiyar muhalli a cikin abubuwan da aka tsara, ciki har da tarin, da yin magani da kuma samun hanyar zubar da ruwan ɗauɗa da na salangogi, abu ne wanda har yanzu ba a samu ci gaban shi ba a Nijar.