An kafa shafin a kan layi a karshen watan Agusta 2020. Yana ƙarƙashin alhakin shugabannin ƙungiyoyihudu na Tarbiyya Tatali.

Gabaɗayan ƙungiyar ta ƙunshi masu sa kai kaɗai.

Tun 2004 Elise Coste ke kulawa da shafi da zane zane na dandalin Tarbiyya Tatali. Amaury Adon ke cigaba da yin gyare-gyaren sigar.

Saïdu da Marie-Françoise Roy suka bayyana abubuwan da ke cikin shafin tun shekara ta 2004 , sannan -bayan 2016 - Marie-Françoise Roy da Seiyaba Elhadj Saïdu , suka ci gaba da aikin bisa takardun ayyukan Tarbiyya Tatali (rahotanni na wata-wata, rahotannin ayyuka, da sauransu). Marie-Françoise ce ta yi aikin rubuce-rubucen da saka su layi har zuwa Oktoba 2020. Yanzu tare da Chantal Blum suke aikin.

Saude Ali Bida ce ke fassara labaran da harshen Hausa . Game da Turanci, Armelle Le Bozec , ce ke yihar farkon 2023 saboda ta yi niyar tsaydawa. Mun yi amfani da kayan aikin fassarar a kai a kai na ɗan lokaci sannan Eva Neveu ta kula da fassarorin Ingilishi tun daga bazara 2024.

Hotunan da ke shafin na Alain Rux, Abdul Aziz Sumaïla, Jean-Pierre Esturnet, Idi Nuhu da Maman Siradji Bakabe ne ko kuma na membobin Tarbiyya Tatali daban-daban.