Asalin ƴan Adam

Ƴan Adam na farko sun bayyana a Afrika ta yamma. Tun zamanin da, shekaru da dama, lokacin da ɗan Adam ya bayyana, wajejen hamada na yanzu, suna da ni’ima sosai, da ba da halayen rayuwa wuri ɗaya. Ana yin ayyukan noma, har birane suka girku.
Abzinawa ko larabawa sun ratsa sahara lokacin da ya koma hamada, cikin ƙarnayen farko na shekarunmu kuma nan da nan hulɗa ta samu tsakanin al’umma farar fata da baƙar fata.

Daulolin Afirka masu ci gaba

Wajen ƙarni na 15 bayan haifuwar Annabi Isa, Sanwayawa na Gawo a ƙasar Mali sun yaƙi sassa tun daga AÏR har kogin Senegal da duka rabin yammacin ƙasar Nijar. Sashen gabas yana ƙarƙashin daular Barnu mai ƙarfi.
Kuma larabawan Maroko da Abzinawa da suka zo daga Fezzan (ƙasar Libiya) sun yaƙi sanwayawa na Gawo. Su ne sabin Mamallaka.
A farkon ƙarni na 19, daular Fulani ta garku daga Sokoto (Cikin ƙasar Nijeriya ta yanzu).

Mulkin mallaka

A ƙarshen ƙarni na 19, Faransa ta yaki ƙasar Nijar, ita ko Biritaniya ta yaƙi ƙasar Nijeriya. Nijar tana ƙarkashin mulkin soja na faransa har zuwa shekara ta 1922 (alif da ɗari tara da ashirin da biyu), Zandar ce babban birni. Bayan Turawa sun mallaki Abzinawa, Nijar sai ta zama mallakakiyar ƙasar Faransa a shekara ta 1926 (alif da ɗari tara da ashirin da shida), Yamai ta zama babban birni.

Kokowar samun mulkin kai

A shekarar 1946, an kafa jam’iyyar siyasa mai suna da faransanci ‘’Parti progressiste nigérien (PPN). Ta haɗa gwiwa da wata jam’iya mai suna ‘’Rassemblement démocratique africain (R.D.A). jam’iyyar ana ce mata GIWA-RDA.Wannan jam’iyya ba ta yarda ba da ra’ayin hukumar mulkin mallaka, daga baya ta yarda da shawarwarin zuwa ga cikakken iko, da ya samu a shekara ta 1956. Jam’iyyar sawaba mai neman cikakken mulkin kai ta yi kira ga dukan ƴan nijar da su zaɓi ‘’a’a’’ ga haɗin giwar al’ummar ƙasar Faransa ga lokacin zaɓan raba gardama na 28 ga watan satumba shekarar 1958. Amma kashi 80 cikin 100 sai suka zaɓi sun yarda da haɗin giwar al’ummar ƙasar faransa. Sai aka hana jam’iyyar siyasar sawaba, jam’iyyar Giwa-RDA ta zama ita kaɗai ce jamiƴyar siyasa cikin Nijar.
Majalisar iyakantacciyar ƙasa sai ta koma majalisar tsarin mulki na ƙasa a ranar 18 ga watan disamba 1958, Bubu Hama yake jagorancinta. ƙasar Nijar ta zama jamhuriya, kuma ta samu ƴancin kai a ranar 3 ga watan Agusta 1960.

Jamhuriyar Nijar

An zaɓi DioriI Hamani, shugaban jamhuriya a shekarar 1960, An sake zaɓar sa a shekarar 1965, kuma a shekarar 1971.
A ranar 15 ga watan Afrilu shekara ta 1974, juyin mulkin soja ya soke majalisar dokoki, ya soke jam’iyyar siyasa, ya naɗa labtanal kanal Saini Kunce sugaban ƙasa. Da ya mutu cikin watan nuwamba shekarar 1987, Kanal Ali Saibu ya jagoranci ƙasar. Bayan gwamnatin riƙon ƙwarya na demokaraɗiya, Mahaman Usman ya canje sa ranar 27 ga watan Afrilu shekara ta 1993.
Tun daga waɗannan zaɓuɓɓuka na demokaradiya, Nijar ta samu shugaba uku. Bayan kisan kai da sojoji suka wa sugaban ƙasa Ba’aré Mainasara, zaɓen raba gardama na ranar 18 ga watan julai shekara ta 1999, ya amince da kundin tsarin mulki na ƙasa. Zaɓen da aka yi cikin ƙa’idoji a ƙarshen shekarar 1999, ya aza Mamadu Tanja shugaban ƙasa a zagaye na biyu.
Cikin disamba shekara ta 2004 (dubu 2 da 4), an sake zaɓen Mamadu Tanja a zagaye na biyu inda ya samu kashi 65 cikin 100, Mahamadu Issufu (Mai jam’iyyar Tarayya) ya samu kashi 35 cikin 100.

A shekara 2009 shigaban ƙasa Tandja Mamadu ya ba da sanarwa, zai zarce da ikon ƙasa. Wannan ya kawo tikass domin taka kunɗin dokar ƙasa. Wannan sanarwa ta sa ƙasa cikin halin yaya za ni yi. Karshen ta dai, Salu Djibo ya yi juyin milki inda ya ce zai maida ma farar hula rikon iko bayan wani lokaci.
Bayan an yi zaɓe sai Mahamadu Issufu ɗan jagoranci adawa bayan shekaru arro arro ya samu samun nadi ranar 12 a watan maris bayan an zaɓe shi da kashi 58 bisa ɗari. An sake zabensa a shekarar 2016 a karo na biyu.

Photo d’Alain Roux