Tarihin Arewa

Tarihin Arewa na dauri, ya danganta da mulki mai alaƙa da addini na mutanen farko aznas tare da Sarauniya, wanda tushen yake a garin Lugu, da Bagagi tare da Baura, da kuma mulkin mayaƙa na Sarkin Arewa wanda tushen yake a matankari .
Zaman ya karkace a lokacin zuwan mulkin mallaka na turawa da suka goyi bayan sarkin Arewa. An yi mamayewar a shekara ta 1899 a lokacin zuwa Turawan da ake ce ma ‘’Vule’’ da ‘’Shanuwan’’ tare da wasu ƙwarorin ’faransawa da sojoji da yawa ɗauke da madafa, bayan da suka mallako wasu yankuna na Afirika. Mayaƙan da Sarauniya Mangu ta sanya don su ceto Lugu da kwari da baka, ba su hana Turawa suka ƙone garin ba, da tarwatsar da mutanen.
Har kullum akwai adawa da mulkin mallaka a cikin yankin.

Addinnan Arewa

Musulunci ne addinin mafi yawan al’ummar Arewa; amma har yanzu tsafi yana da saura. Gumakka ne suke taƙaice tarihi da al’adun, da Doguwa mai kariyar al’ummar azna idan an yi mata yadda take so, ko kuma ta yi ɓanna idan aka mance da ita. Yanzu addinin azna ya koma kan bori inda kowa yake da aljannunsa. Ana samun masu addinin kirista kaɗan, kuma ana rayuwa tare a cikin kwanciyar hankali.

Al’adun gargajiya na Arewa

Akwai wata al’ada ta masamman a Arewa. Ita ce ta daidaitaka tsakanin maza da mata a kowane fanni, kamar in aka dubi ikon Sarauniya ta Lugu Abin da muke sa ran yi.
Bayan abubuwan ƙasƙanci da na wulaƙanci da suka faru a lokacin zuwan turawa ƴan mulkin mallaka, a yanzu abin da mu muke sa ran yi, shi ne wata haɗuwar, amma ta alheri, ta cuɗayya da girmama juna, da jittuwar al’ummar yankin.

Ayyukanmu da tsare-tsarenmu wajen al’adu suna da yawa.

Accueil azna

 

Dans cette rubrique