Muhimmancin gatannai cikin tsarin horo na al’ada

A Nijar, har kullum gatanna tana da muhimmici cikin tsarin horon yara.
Ana tsarin horon yin gatannai ta hanyar cewa : ba abu mai kyau ba ne zaluntar masu rauni, don son zalunci ga wasu, yara su kasance masu son zuciya, su yi wa iyaye ko yara ba’a, amma ga akasin haka, cewa wajibi ne mu saurari tsofaffi masu hikima, girmama mahaifinsa da mahaifiyarsa, don taimaka wa maza da mata masu matsalolli ...

Misalai huɗu na gattannan Nijar

Hanyar gama kai da aiki tare

Littatafai guda biyu na Tarbiyya Tatali, sune sakamakon wani shiri na gama kai masu yin gatannan, su ne : malamai, dalibai, mutane da yawa ne suka kawo gudunmuwarsu wajen yin su.

Za ku iya sayan littafinmu wanda aka buga a shekara ta 2009 “Wani lokaci can a Nijar” a kantinmu.
wani ɗan Nijar ya kula da zana hotuna, wasu malaman makaranta na Nijar da na Faransa suka ƙara aikata matannai, wani kuma ya kula da tsara littafin. Gaisuwa ta masamman zuwa ga Nilo Royet saboda yin siffar littafin, zuwa ga Isufu M’barke Wali da Dominique Berlioz da suka rubuta matannan faransanci, da Saude Ali Bida da ta fasara wasu matananan hausa zuwa faransanci.
An yaɗa littafin a Faransa da Nijar, Kuma kuɗin da aka samu daga sayar da wannan littafi na taimakawa ga ayyukan Tarbiyya-Tatali a Dogon Dutsi.
Littafin da ya gabata “A makarantar gatannan Nijar,” wanda aka buga a shekara ta 2004 ya kare, wato an sayar da shi duka

 

Dans cette rubrique