Wannan gatanar ta fito daga littafinmu na gatannai mai sunan ‘’il était une fois au Niger’’ a turance, wato « Nijar, a wani lokaci’’. Kuna iya samun littafin a cikin kantinmu.

Kokowar dabbobi

A lokacin da dabbobi suke yin kokowa tsakanin su ne. Kamar yadda aka saba yi, bayan an fidda amfanin noma, sai aka shirya wata kokowa a garin. Daidaya, makaɗin garin yana buga gangarsa a tsakar filin kokowa cike da ƴan kallo, yana yi wa Damo kirari, yana cewa:

  • Kai Damo abokin sure da daudawa( har sau biyu).

Sai Damo ya riƙa cika, yana kumburi, yana sacewa, yana ɗaga wutsiya sama a tsakar ƴan kallo. Da ganin haka, sai Gizo-Gizo ya so yin kokowa da Damo don ya nuna iyakar ƙaryar Damo. Sai Damo ya fara gayi da ƙarfin murya, yana cewa :

  • Kai, Gizo-Gizo mai awazzu a fili, fita daga nan ! je ka nemi warinka tunda ni ina iya murje ka. Damo ya ci gaba da ɓaɓatu.

A cikin ƴan kallon, wasu suna cewa kokowar ba ta dace ba ; ƙarfinsu bai zo ɗaya ba. Wasu kuma suna neman a yi kokowar don marasƙarfi ya san warinsa. Shi kenan, sai ƴan kokowar biyu suka shiga fili, alƙali ya busa. Kowa ya yi tsit ; ko lumfashi ba a ji. Kokowa ta turniƙe sosai, ana juye-juye da goce-goce. Damo yana neman ya murje Gizo-Gizo da ƙarfi, amma da lauɗinsa sai Gizo ya haye bisa bayan Damo. Gardama ta taso ; wasu suka ba Damo kaye, wasu kuma suka ba Gizo-Gizo. Ganin haka, sai aka maida su fili don su sake yin wata kokowar. Yanzu ma da sauri, sai Gizo ya haye bayan Damo, kuma Damon ya rasa yadda za ya yaddo shi ƙasa. Duk da haka, magoya bayan Damo suka ce sai an sake kokowar. Wanga karon ma Gizo ya ci nasara.
A nan ne kuma, daga can ƙolin wurin ƴan kallo, sai kurciya ta ce wa shaho :

  • Yanzu ni ce za ni yin kokowa da kai tunda na ga yadda Gizo ya yi wa Damo.

Jin haka, sai suka fara cewa :

  • Ba a san maci tuwo ba sai miya ta ƙare.

Babu ɓarnar lokaci, sai kokowa ta fara. Daga saƙƙwatar baki guda, sai shafo ya kame wuyan kurciya, ya shaƙe, ba tare da an ji abin da take faɗi ba a wannan lokacin.
Aka zaburo ana neman raba kokowar, ana cewa mugunyar kokowa ce mai hatsari ; ba ta dace ba (sau biyu). An tsaida kokowar, amma har wuyan kurciya ta ƙare a lokacin nan ; sai ta mutu daga baya. Shafo ya fara cewa :

  • Kin nuna mini matuƙar reni, kurciya. Hakan ya ishe ki darasi.

Abin aƙida shi ne : A duniya, ka ba kowa darajarsa, kuma kowa ya san sa’ansa (warinsa) a cikin jama’a.

Makarantar boko ta Isakici Mai gatana : matar marigayi Gaya Maƙeri rukunin ƴan makaranta : Abdu-Rahaman Soba, Asuman Bawa, Nuru Bubakar, Mumuni Hasan, Nuru Hasan, Idi Saidu mai kula da tsarin : malam Karimu Isa, shugaban (Daraktan) makarantar.

Il était une fois au Niger