Kawo mana goyon baya

Gudunmuwar da kuke iya kawo mana, ita ce kulawa da harakokin Nijar da Afirika; ku goyi bayan ayyukan ci-gaba mai ɗorewa da muke yi, da na cuɗayyar al’adu, da na taimakon juna. Abokanmu na Nijar masu gudanar da aikin Tarbiyya Tatali, suna buƙatar goyon bayanmu da ra’ayoyinmu a duk lokacin da suke tsare-tsaren ayyukan ci-gaba.

Da kuɗi kaɗan akan yi abubuwan mamaki

Ƴan kuɗi kaɗan idan an sanya hannunsu, sun ishe su aiwatar da ayyukan a-zo-a-gani. Kuɗin yuro 2 (kimanin jika 1 da 60) suke sayen littattafan ƴan makaranta na yaro 1 ; yuro 10 (jika 6 da rabi da dala 11) sun isa abincin rana na yaro 1 har tsawon shekara. Yuro dubu 4 da ƙungiyar take tattarawa, sun isa aikin ajin ‘’Espoir’’ na shekara 1, da biyan malaman makaranta na shekara 1, ko kuma biyan shekara na babban malamin likita. Moton ƙungiyar ta tashi yuro 1200, kuma motar da ake amfani da ita don ziyartar ɗakunan shan magani na garuruwa, ita kuma ta tashi a yuro 7000.

Gudunmuwar kuɗi

Gudunmuwarku ta kuɗi ko ƙaƙa, tana da babban amfani kodayaushe ; Idan kuma kuna so, kuna iya faɗin aikin da kuka kawo ma goyon bayan, ko kuma ta hamyar sayen abubuwan da muke sayarwa a kantin Tarbiyya Tatali.

Shiga ƙungiyar

Idan kuna buƙatar ku raka mu, sai ku shiga ƙungiyar AECIN, AESCD.

Ku keɓe wani lokacinku saboda mu

Ko kun shiga ƙungiyar ko ba ku ciki, idan kuna da isasshen lokaci, to ku keɓe mamu kaɗan domin sanar da abubuwanmu a kewayenku, ko samo hanyoyin taimaka ma ayyukanmu a ma’aikatarku ko wurin hukumarku, ko kuma sanya baki wajen nuna ingancin wani daga cikin tsare-tsarenmu.

Photo d’Alain Roux