Yawan mutane da haihuwa

Nijar na samun ƙaruwar yawan mutane kamar kashi 3.9 bisa ɗari a kowace shekara, a kan haihuwa kuma ko wacce macce tana da kamar kimanin yara 7.6.

A shekarar 2012 lissafin mutane ya gano da cewa su ne mafi yawa a duniya kuma adadinsu na ta karuwa.
mace-macen Jarirai ya rage amma karfi adadin ​​haihuwa na ta karuwa, a cikin ma har da halin aurar da mata da wuri (kashi 30 bisa ɗari na mata ake yi wa aure kafin shekaru 15), da na zama da kishiyoyi (macce kashi 36 bisa ɗari na da kishiya).

Karuwar yawan jama’ar ƙasar da miliyan 5 a shekarar 1970 zuwa sama da miliyan 20 a shekarar 2018 ya fi na ci gaban tattalin arzikin kasa, kuma tattalin arziki na ‘yan ƙasa ya fadi zuwa kashi 40 bisa dari tsakanin shekarar 1970 da shekarar 2012.

En 2017, le taux de croissance démographique est estimé à 3,2% avec un taux de fécondité de 6 enfants par femme.
Selon l’Enquête Démographique et de Santé du Niger 2017, la baisse est plus importante dans la région de Dosso , ­passant de 7,5 à 5,7 enfants par femme.

Inganta tsarin iyali

Ma’aikatar Lafiya ta soma wani shirin (2012-2020) domin taimakawa wajen samun saukin yawan mutane na inganta tsarin iyali. Manufar shine a matsa daga kashi 11 bisa ɗari na zamani maganin hana haifuwa zuwa kashi 50 bisa ɗari dangane da dabarun uku na tsarin iyali.

  • karfafa samar da kiwon lafiya cikin likitoci
  • karfafa bukatar ta hanyar ilimi da kuma wayar da kan jama’a
  • gabatarwa na wani yanayi mai dama.

Samun tsara wannan dai na bukatar janyo ra’ayoyin jama’a na musammun.

Sakamakon farko

A shekarar 2017, an kiyasta yawan karuwar mutane zuwa 3.2% tare da yawan haihuwa na yara 6 ga mace daya.
A ra’ayin ƙungiyar binciken alkalumma da kiwon lafiyar Nijar na shekarar 2017, raguwar ta fi muhimmanci a yankin Dosso, daga yara 7.5 zuwa 5.7 ga mace ɗaya.

Tsafi

  • Enquête démographique et de Santé à Indicateurs Multiples du Niger 2012 (INS et ICF International)
  • Les défis démographiques des pays sahéliens, J. F. May, J.P. Guengant, Études, 2014