A can baya, a ƙarshen karatu, gurin kowa shi ne na zama ma’aikacin gwamnati.
Amma yanzu da lokaci ya sauya, ya kamata gurori su sauya a ƙarshen karatu.
A ra’ayin Tarbiyya Tatali, ya kyautu mutum ya yi karatu don kanshi, don gane al’amurran duniya da yin amfani da su a zamantakewar ƙasa da tattalin arzikinta.
Ga gurorin da ya kamata :
Mutum ya iya karatu da rubutu,
- da ƙilgo ko fasali a cikin harshen gida da faransanci,
- da sanin yadda jiki yake ciki, da iya tsabta,
- da gudanar da ayyuka masu amfani,
- da iya sadawa da al’umma,
- da sanin al’adunsha,
- dudewa ga duniya.