An kammala wannan mataki.

Hanyar riƙe ƴan mata a makarantar kwaleji

A Nijar, ƴan mata ƙalilan ne suke samun kammala karatunsu na kwaleji.
Dalilin haka shi ne yawan aikace-aikacen gida da suke fama da su idan aka kai su zama a wasu gidaje daban, tunda babu makarantar kwana inda za a tara su.

Wannan matsalar, an shawo kanta game ƴan matan garin Bagaji ta hanyar gidan Fadu, tamkar makarantar kwana inda yan matan suke a cikin wadataccen halin tafiyar da karatunsu.

Al’ummar garin Badaji da ta garuruwan kewaye, sun tashi tsayin daka ga gowon bayan wanga tsarin wanda matan ƙungiyar AECIN, da mutane ƴan asulin garin Bagaji suka zuba kuɗin girka shi, tare da taimakon ofushin Ministar horo ta hanyar koyar da sana’a, da kuma tallafin ƙungiyar taimakon al’umma.

Tun watan Mayu zuwa juni na 2009 aka ƙare ginin makarantar kwanan ; amma har a farkon watan Disamba ba a buɗe ta ba, tunda kwalejin garin Bagaji ba ya bada sakamakon da ake so : a cikin ƴan makaranta 14 na farkon jarrabawar Birebe (BEPC a turance) a shekarar bara, ɗaya (1) tal ya ci nasara ! Hakan ya kashe wa uwaye lakka kuma ya rage hamzarin buɗe makarantar kwanan.

Wai wace ce Fadu ?

A tarihin Arewa, Fadu, ɗiyar Baura ce kuma jikanyar sarauniya. Ta auri wani ɗan sarkin Bornu mai suna Ari inda ta haifi Akazama, sarkin Arawa na farkon, da abokin tagwaicinshi, Ganci. Bayan tafiyar Ari, ta yi aure da yawa inda ta samu wasu ɗiya, su ne : sarkin ruwahi, da sarkin lahama, da sarkin Tudu, da kuma sarkin yamma Ligido.

Kenan ita dai ce uwar al’ummar Arewa baki ɗaya, kuma haɗin kan ƴan jahar Arewa.

Halin da ake ciki a lokacin zafi na 2010.

Ta hanyar ƙoƙarin matan ƙungiyar AECIN, da tallafin kuɗin de Rotary Club na birnin Rennes ya bayar, an samu buɗewar makarantar kwanan ƴan mata a cikin watan Mayu na 2010. Ƴan matan sun fito daga garuruwan kewayen Bagaji ; su ne : Rumbuki mai nisan kilometer 14, da Rijiyar Maida (kilo 15), da Salga (kilo16), da Gezanya (kilo 6), da Tumfafi (kilo 15), da Maƙera (kilo 17), da kalgo, da Bagaji da kanta. Ita makarantar kwalejin Bagajin ta ƙumshi ƴan makaranta 250. A cikin su, kashi 30 bisa 100 ƴan mata ne.

Wani mai tebur da ake ce wa malam Bori, shi ne dukan uwayen ƴan makarantar garin Bagaji suka ɗora wa nauyin tsaron ƴan matan. Kafin buɗewar makarantar kwanan, a kasuwa ne yake aza teburinsa. A yanzu kuwa, sai ya maida shi bakin ƙofar makarantar kuwanan don ya samu dammar kula da ƴan matan dare da rana.

Wasu malaman makaranta sun kawo gudunmuwarsu ta hanyar bada ilimin lissafi, da Ingilishi, da ilimin kimiyya, kuma wasu mata masu horarwa suka dafa masu baya, su ma.

An samu ƙarin hamzari kaɗan tunda ƴan makaranta 8 suka ci nasara ga jarrabawar ƙarshen karatun kwalijin Bagaji cewa ‘’Brebe’’ ; sai dai babu mace ko ɗaya a cikin waɗanda suka ci nasarar.

Gidan kwana a shekara 2011 zuwa 2011

Ƴan mata talatin ne a gidan daga 2010 zuwa 2011, da tallafin uwayensu wajen abinci ( hatsi da ke abincinsu na tushe) da kuma taimakon kuɗi na Rotary Club na birnin Rennes Broceliande.

A shekarar 2011 ƴan makaranta 8 suka ci nasara ga jarrabawar ƙarshen karatun kwalejin Bagaji wato ‘’Brebe’’ ; sai dai babu mace ko ɗaya a cikin waɗanda suka ci nasarar.

Aikin koyarwa daga 2011 zuwa 2012

Ganin rishin ci nasarar ƴan mata a jarabawar ƙarshen kwaleji, wato brebe, da kuma wuyar samun kuɗin tafiyar da gidan kwana da na aikin koyarwa, an ɗauki shawarar ba da ƙarfi a aikin koyarwar da ƴan mata na ajin ƙarshen kwaleji, saboda samun cin nasara ga jarabawar brebe. Saboda wannan an soƙe aikin gidan kwana daga 2011 zuwa 2012.

Amma ana kwas dayawa don ƴan mata na ajin ƙarshen kwaleji lokacin hutu. Bisa ƴan mata 26 da ke akwai a ajin, 23 ne suka yi wannan kwas ɗin na farko sosai a ƙarshen shakarar 2011.

Ƴam matam kwaleji uku na Bagaji suka ci nasara ga jarabawar ƙarshe ta kwaleji, tare da yara maza hudu. Adadin ƴam matam da suka ci wannan jarabawa tun da aka ƙera kwalejin a shakarar 2007. Daga ko ɗaya an samu uku kenan.

Wannan niya ta samu tallahinta daga dangatacen hadin kai mai mahimmancin ra’ahin ikau na ƙungiyar tatalin ɓunkasar ci gaba na Faransa da ke tanadin talahwa ma waɗanda suka dace ta dattata hangna RESDEN. Wannan ƙungiya ta RESDEN ta kan zaɓi ƙungiyoyin da suka dace kuma ta kan kula da yadda suke wakana.

A watan yuli na shekara 2012, yan mata uku na kolejen Bagaji suka samu digrin brebe bayan gama karatun shekaru huɗu. A panin maza, samari huɗu ne suka dace samun wannan digri. Wannan shi ya kawo raskonna cewa tun kafa wannan koleje, yan mata uku sam ne suka samu wannan yabo na digri brebe.