A Dogon Dutsi, gidan Matasa da na Al’adu mai sunan Yazi Dogo yake. A yanzu dai ayyukan ta kadan ne, sadoda rishin hali dayawa. Tarbiyya Tatali tana da tsari na raya gidan zarafi na al’adun Arewa. Tara abubuwa musammun ma bisa Yazi Dogo sa hannu ne cikin kafa wannan tsarin.

Wane ne Yazi Dogo

Malamin makaranta ne, amman an fi sami shi a matsayin ɗan wasan kwaikwayo a nan Nijar : ɗan wasan kwaikwayo, mawallafi, marubuci. Ya rubuta wasan kwaikwayo kamar talatin, da kuma almara kamar ɗari. Gidan radiyo da talabijin ta Nijar ta fara wallafa su a shekarar 1978.

Wasan kwaikwaiyon dai cikin halshen faransanci, da hausa wadda take halshen uwar shi yake yin shi.

An haife shi dai wajan shekara 1942 a Maizari, cikin yankin Dogo Dutsi, yanzu ya yi ritaya.

Yana ci gaba da shugabantar da « ƙungiyar Yazi Dogo ».

A cikin tarihin al’adu yake samun labarun wasan kwaikwayon (kamar labarin sarki mai baƙi rai Kabrin Kabra da ya so ya kashe tsofi duka), ko kuma cikin labarun yau da kullum (kamar yaki game da cin hanci) da kuma wasannin na ban dariya, saboda mutane suna son dariya dayawa a ƙasar hausa.

Yana kuma kawo gudummuwar shi wajen ci gaban mutuncin halin mata (kamar zuwa makarantar ‘yan mata, arme dole ko na ‘yan mata ƙanana, da samun sarari wajen haifuwa, da rishin abinci mai gina jiki) ko kuma cutar karayar garkuwar jiki, ko shan-inna…

A duba nan don ƙarin bayani.

Ƙarin bayani bisa Yazi Dogo

An yi ayyuka dayawa bisa aikace_aikacen Yazi Dogo, kamar wata tattaunawa da videon, a ciki dai, membobin ƙungiyarmu sun kawo gudummuwar su sosai.

Tattaunawa tsakanin Yazi Dogo da Jean-Dominique Penel
A yi shi ran 22 ga watan october 1989, an wallafa shi cikin kashi na « Rencontre, Littérature nigérienne », Editions du Ténéré, édité par J.-D. Penel et A. Maïlele.

Videon da Joanna Cussigh ta yi


Yazi Dogo par PromoChabrol

Video ne mai tsawon minti 20 mai sunan « Yazi Dogo et le théatre populaire nigérien » Joanna ta wallafa shi a ziyarta ta cuɗayyar juna a Nijar cikin shekara 2010.

Yazi Dogo