An kammala wannan mataki.

Matan yankin Arewa sun yi wani taro a garin Lugu, wanda shi ne na farko a ranar 13 ga watan mayu 2005, ranar sallar mata na Nijar baki ɗaya.

A irin wannan ranar ce ta shekarar 2007, matan Arewar suka yi niyyar su yi yabo na masamman ga wasu mata waɗanda suka nuna ƙwazo da himma domin kyautata matsayin matan Nijar.
Sarauniya Aljimma da Ministar ci-gaban mata da kariyar yara, su ne suka damƙa wa waɗannan matan shaidar yabon girman. Matan guda 4, waɗanda suka nuna hali irin na sarauniyar, sun samu wani kwali wanda ya ƙumshi ƙwallon zaren sarauniya Aljimma, shaidar ƙwazonta don jin daɗin rayuwar al’ummarta, da hoton ɗan dutsin da ake kira Tunguma, shaidar gaskiya da adalci. Bayan haka, Tarbiyya Tatali ita ma ta yi murnar yi musu kyautar wannan littafin mai suna ‘’Lugu da sarauniya’’ a fasarce, mai bayyana al’adun al’ummar azna.

Matan da suka samu kyautar yabon, su ne :

Madame Aïchatou Mindaoudou

Sunanta ya fito masamman a lokacin tattaunawa da irin rawar da ta taka ga shari’ar da ta damƙa ma ƙasar Nijar dukan ƴancin mallakar tsibirin da ake kira ‘’Ile de l’été’’ tsakanin Nijar ɗin da ƙasar Benin. Ta yi shugabanci da yawa, kuma sau biyu kenan take kama matsayin Minista.

Madame Foumakoye Nana Aïchatou

Akwai mai ɗakin malam Fumakwai, cewa da malama Nana Aishatu ; ta sha gwagwarmaya don ci-gaban mata, masamman ma matan karkara. Ta yi Minista, kuma ita ce ta yi dalilin ɗaukar dokar da ta ƙara ma mata yawan wakilai a majalisar dokoki a shekara ta 2004, inda daga mace 1 tal, aka kai har mata 14.

Madame Moumouni Aïssata

Sai kuma mai ɗakin malam Mummuni cewa da malama Aisata. Ita ce mace ta farko da ta zama Minista. Ta buɗe wa ƴan uwanta mata hanyar ɗaukar babban matsayi da shugabanci a fannin siyasa, waɗanda maza kawai ne suke riƙe da su a can baya.

Madame Mounkaïla Aïssata

Sai mai ɗakin malam Munkaila cewa da malama Aisata.
Tana ɗaya daga cikin matan da suke yaƙin ganin ana kyautata wa mata cikin dukan harakokin ƙasa. A Nijar, ita kaɗai ce macen da ta zama ƴar majalisar dokoki, wato « Dipite » har sau 4.

Duka waɗanga matan 4, sun taka mahimmiyar rawa a matsayin shugabanni, wajen neman ci-gaban matan Nijar, da kuma kokowar da ƙasar Nijar take yi don fita daga sahun ƙasashe matalauta.

Fête à Lougou le 13 mai 2007
{{}}