Kuna iya sayen « Tarihin Kwanawa » a kantinmu or on the website of l’Harmattan.
Tarihin Kwanawa, Tarihi da al’adun tsofi.
Wannan littafi an yi shi ne tare da haɗin giwar L’Harmattan, Tarbiyya Tatali kuma ta gabatar da tarihin Kwanawa na jihar Dogondutsi, a ƙasar Nijar. Yana ƙumshe da tarihin baka dayawa da aka samu wurin mutane. A cikin wannan littafi ana iya ganin abubuwan da suka haɗa mutane da al’adun galgajiya na ɗa, tahirin tsarin mulki iri iri tare da sa hannu sarauniyar Daura da ta Lugu, tarihin kuma ya ci gaba har wannan zamani, tare da bin sau da sau lokacin mulkin mallaka da lokacin mulkin kai.
Muryar tsofi, shi ne babi na karshe na littafin an ba da bayani bisa masu ba da labarai 3 da hulɗar da ke tsakaninsu da marubucin. Littafin ya kare da ba da kuzari wuri sauran wakilan jama’a da su yi irin wannan littafin.
Marubucin
A haifi Dangaladima Issa-Danni Sumana a shekarar 1952, ya yi karatu a makarantar « mission » ta masu gemu a Dogondutsi. Baya karatu na sakandare da na ƙoli a Burkina Faso da Nijar, ya zama mallamin turanci a kwalejin Yamai da Dogondutsi, kuma ya zama daraktan kwalejin Tchintabaraden da na Bilma. Daga shekara 1984 zuwa 2006 ya shugabanci ofis na jarabawa a ma’aikatar ilimi kuma a gidan hanyar ilimi ta sakandare ta Yamai.Tun shekarar 2006, ya yi ritaya. Babban member ne na kwaminin kwanawa, ya san asirinsu dayawa game da amanar da ke tsakaninsu. Ya ba mu wannan taƙaitacen labari bisa sakamakon bincikensa.