A cikin watan Juli na 2010, Gidauniyar ‘’Stromme’’ da ‘Kungiyar RAEDD sun raba buhu 1000 na hatsi masu kilo 35 kowanne a cikin kwaminonin dapartaman Dogon Dutsi inda ke akwai tsarin makarantun buɗe hanyar ci gaba da karatu ‘’classes passerelles’’, da tsarin ‘’tsimi don kawo canji’’ wato ‘’Epargne pour le changement’’. Bayan an shawarci al’ummar da abin ya shafa, sai aka ke’be waɗanda za a fi ba fifiko. Su ne : mata masu ban nono, iyalai mafi ƙaramin ƙarfi, da ƴan makarantar makarantun buɗe hanyar ci gaba da karatu, da matan da suke cikin tsarin ‘’Tsimi don kawo sauyi’’.

A shekara ta 2016, ruwa sama sun faɗi sosai a karkara Dankatsari.

A 26.08.2016, an gano da cewa gonaki masu faɗin ha 198,3 da na lambuna 4 (Kamrey, Houda Masari, Mailo, Dankatsari), da rijiyoyi hudu sun lalace (uku masu amfani biyu : wajen dabbobi da kyauyuka, da wata rijiyar kauye). Idan an haɗa su kenan ya safi shugabannin 131, bisa yawan mutane kamar 1477.

Game da shawarar RAEDD, AESCD da AECIN sun taimaki iyalan da suka rasa amfanin gonakinsu gaba daya, sun ba su buhuna 50 na kilo 100.

Distribution aux mères allaitant